Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta gabatar da ma aurata biyu gaban kotu bisa zarginsu da cin zarafin yara.
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta kama tare da gabatar da wasu ma aurata gaban kotu bisa zarginsu da cin zarafin yara kananan.
Ma auratan Wanda suka hada da Fatima Abubakar yar shekaru 28 da haifuwa tare da mijinta Abubakar Yuguda wadanda ke zaune a anguwar Sanda makam B dake cikin karamar hukumar Yola ta kudu wadanda ake zarginsu da cin zarafin yara kanana dake karkashinsu.
Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola.
Wadanda aka ci zarafinsu dai sun hada da Hapsat Abubakar yar shekaru 2 da haifuwa da Usman Abubakar Dan shekaru 4 da haifuwa Wanda Kuma yadukonsu ce ta shiga gasa musu Aya a hanu kafin daga bisani Jami an Yan sanda suka cetosu.
An samu nasaran kama wadanda ake zargine biyo bayan rahoton da makwamtansu suka kawo Wanda Kuma hakan yasa aka cigaban da bincike dangane da lamarin.
Tunin dai wadanda ake zargin suka amsa lafinsu hakan yasa aka gabatar dasu gaban kotun majistare 2 dake Jimeta domin su fuskanci shariya.
Kwamishin nan yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya jaddada aninyar rundunan na cigaba da kare rayuka dama dukiyoyin Al umma musammanma yara, ya Kuma tabbatar da cewa za ayi musu adalci, ya kirayi Al umma da sukasance masu Kai rahoton duk wani cin zarafin yara ga hukumar Yan sanda domin daukan matakin akai.
Comments
Post a Comment