Rundunan Yan sandan jahar Adamawa Tasha alwashin inganta tsaro a fadin jahar.

 






Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin inganta tsaro a lokacin dama bayan watanni Emba.  A fadin jahar baki Daya.




Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ne ya baiyana haka a wata sanarwa da kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya rabawa manema labarai a Yola.





Sanarwan ta baiyana cewa kwamishinan ya umurci Jami an yan sandan karkashin rundunan dake yaki bata gari wato Crack da su bazama su baza komarsu domin kama tare da hukunta duk Mai kawowa zaman lafiya barazana a tsakanin Al umma.




Kwamishinan ya Kuma baiyana cewa yin haka zai taimaka wajen dakile duk wata fitina da kan  iya tasowa akan lokaci ba tare da an samu matsalaba.





Harwayau kwamishinan Yan sandan ya umurci dukkanin manyan Jami an dake ofisoshin Yan sandan dake fadin jahar dama kwamandodin Yan sandan da su tabbatar sun dakile aikata laifuka a Yan kunansu.





Kwamishin yace rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma, saboda haka rundunan tana bukatar hadin Kai da goyon baya tare da Kai rahoton dukkanin abinda basu aminta da Shiba ga ofishin Yan sanda mafi kusa domin daukan matakin gaggawa akai.


Rundunan ta Kuma rarraba wayoyin domin kira kamar haka, 08089671313, 08130013347,

08030693476,

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE