Rundunan Yan sandan Najeriya ta kudiri aniyar inganta tsaro a fadin kasar.

 






A kokarinta na Kara kaimi wajen inganta tsaro dama kare rayuka da dukiyoyin Al umma, hakan yasa Babban sifeton Yan sanda Najeriya Kayode Egbetokun ya gudanar da taro da mataimakan sifeton Yan sandan na shiyoyi,ad  kawamishinonin na jihohi domin tattauna tare jaddada Kara kokarin ganin abi doka da oda a fadin kasan nan.





Kakakin rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.







A lokacin tattaunawar Babban sifeton Yan sandan Najeriya ya baiyana irin nasarori da rundunan ta samu a lokacinda take gudanar da aiyukanta na yaki da masu fashi da makamai, masu garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa,dama sauran lafifika. Don haka nema ya bukaci Jami an Yan sandan da sukasance masu tabbatar da kare Al umma.




Babban sifeton ya Kuma shawarci manyan Jami an Yan sanda da su Kara kaimi wajen ganin anbi doka da oda da Kuma maida hankalin da baiwa Al umma kariya domin ganin an samu nasaran gudanar da aiyukan rundunan yadda ya kamata ga Al umma.




Dan gane da zaben gwamna jahar Omdo da ake Shirin gudanar a ran 16-11-2924 Babban sifeton yace rundunan a shirye take wajen yin amfani ta kwarewa domin ganin anyi lafiya ba tare da matsalaba.




Babban sifeton ya Kuma sanar wa manyan Jami an Yan sanda cewa za a gudanar Babban taro a ranar 25-28-11-2923 a Abeokuta fadar gwamnatin jahar Ogun. Inda za a tattauna batutuwa da dama.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.