Rundunan Yan sandan Najeriya ta taimakawa Jami an Yan sanda 16 da hatsarin mota ya ritsa dasu a tsakanin Kano da Zariya.

 







Rundunan Yan sandan Najeriya ta taimakawa iyalen dama Jami an Yan sanda da suka gamu da tsarin mota akan hanyarsu ta dawowa daga zaben gwamna da akayi a jahar Edo biyo bayan da suka gudanar da aiyukan na musamman a lokacin Zabe.




Hatsarin dai ya ritsa da Jami an Yan sanda 16 Wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar 5 daga cikinsu goma Sha Daya Kuma sun kwanta a asibiti Wanda kawo yanzu an Sami 8 daga cikin sai dai Jami an uku suna cigaba da karban Magani a asibiti.



Hatsarin dai ya farune akan tagwayen hanya da suka tashi daga Zariya zuwa Kano.




Mai Hulda da jama a na rundunan Yan sandan na kasa  ACP Oumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.




Sanarwan tace biyo bayan aukuwar lamarinne sai Babban sifeton Yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya taimaka da kudade ga iyalen Yan sanda 16 da hatsarin ya risa dasu ga wadanda suka rasa rayuka wato Jami ai 5 kowanensu an baiwa iyalensa nera Milyon goma, sai Kuma wadanda har yanzu suna kwauce a asibiti a baiwa kowannensu nera Milyon  2 sai Kuma wadanda aka sallamesu su Kuma kowannensu ya samu nera dubu Dari biyar. Su da du dai jimlan kudin nera Milyon sittin ne.




Tunin dai Babban sifeton ya umurci sashin inshora da kasafin Rundunan da ya ganatarwa wadanda suka amfana da taimakon domin samun walwalan Jami an tare da tabbatar da cewa za a biyar kudaden na tare da ninkiriba.



Babban sifeton yace rundunan a shirye take ta cigaba da kula da walwalan Jami an Yan sandan domin Kara musu kwarin gwiwar inganta aiyukansu na kare rayuka dama dukiyoyin Al umma baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE