Wani matashi da ake zargin da yunkurin hallaka kansa ya shiga kamar Yan sanda a jahar Adamawa.

 





Hukumomin Yan sanda a jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da wani matashi Mai Suna Abdullahi Muhammed Mai shekaru 30 da haifuwa Dan karamar hukumar Gashaka jahar Taraba.




An kama matashin ne bisa zarginsa da hallaka kansa a karamar hukumar Mayo Belwa dake  jahar Adamawa, ana zargin matashin ne a lokacinda yayi yunkurin kama Tiransifoma Mai karfin 33kv dake tsakanin Yola zuwa Jalingo.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Sanarwan ta Kuma baiyana cewa daga Jin labarin haka kwamishin yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya umurci jami an  Yan sandan ofishin Yan sanda dake karamar hukumar Moyo Belwa da su garzaya wurin sai akayi Sa a aka sameshi Yana kokari hallaka kansa yanzu haka Yana hanun Yan sanda domin cigaba da bincike Kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.




Sanarwan ta Kuma baiyana cewa rundunan yan sandan a shirye take wajen kare rayuka dakum dukiyoyin Al umma ciki harda wadanda ke kokarin hallaka kansu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE