Wasu da ake zargi da aikata laifuka sun shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa.
A kokarinta na inganta tsaro da Kuma dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar Adamawa rundunan Yan sandan jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da wasu matasa hudu da ake zargin da addabar anguwar Jambutu dake cikin karamar hukumar yola ta arewa dake jahar Adamawa.
Anyi nasaran kama wadanda ake zargine a mahadar Geriyo da misalin karfe 2:00 am wato da dare Kuma an kama su da makamai masu hatsari da suka hada da wukake harma da tabar wiwi da dai dai sauransu.
Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SL Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Hakan na zuwane bayan koke koke da ake samu nayin fashi da makamai da sace sace da ake samu a cikin Al ummar yankin Kuma a yanzu haka wadanda ake zargin suna hanun Yan sanda domin cigaba da bincike.
A sanarwan anjiyo kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Dankwambo Morris ya tabbatar da cewa rundunan a shirye take ta cigaba da kare rayuka dama dukiyoyin harma da inganta tsaro ga mazauna fadin jahar.
Comments
Post a Comment