An bukaci da Al ummah sukasance masu hada kansu da Kuma hakuri da juna.
An bukaci Al umma musulmai sukasance masu maida hankali wajen karatun Al Qur ani Mai gurma tare da tura yaransu makarantun Islamiyoyi da makarantun zamani domin Samar da hadin Kai da Kuma cigaban addinin musulunci.
Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ne ya bukaci haka a lokacin da yake jawabi a wurin bikin bude gasar karatun Al Qur ani Mai gurma da ya gudana a karamar hukumar Demsa dake jahar Adamawa.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Wanda kwamishinan kananan hukumomi da masarautu Hon. Ibrahim Yayaji Mininyawa ya wakikta ya jaddada cewa shirya irin wannan gasa a tsakanin Al umma musulmai Wanda hakan zai baiwa matasa damar fahintar Al Qur ani Mai gurma yadda kamata.
Gwamnan ya yabawa wadanda suka shirya gasar Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa karatun Al kur ani Mai gurma a tsakanin Al ummah.
Da yake jawabinsa na maraba shugaban kwamitin shirya gasar Alhaji Aliyu Isma ila Numan ya godewa dukkanin wadanda suka jalaci taron tare da shawartan su da sukasance masu hakuri da juna a Koda yaushe domin samun cigaba harma da wanzar da zaman lafiya
Ya Kuma shawarci daluben gasar da sukasance masu baiwa shuwagabannin hadin Kai domin ganin an samu nasaran gasar.
Har wayau ya kirayi Alkalain su gudanar da adalci da tsaron Allah a lokacinda suke gudanar da aiyukansu domin Samar da zaman lafiya da cigaba.
Da yake gabatar da mukala a wurin bikin Dr Bashir Aliyu Imam Hong wanda Dr Aminu Yakuma Babban Limamin Masallacin Jumma a na Daya dake Nasarawa Damsa ya wakilata ya zaiyani irin muhimmanci da karatun Al Qur ani yake dashi ga Al umma musulmai, saboda haka nema ya shawarci al umma musulmai da sukasance masu Neman ilimi Al kur ani Mai gurma.
Anshi bangaren shugaban majalisar harkokin Addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ya baiyana farin cikinsa da godiyarsa dangane da Hamman Batta Gladstone Alhamdu Teneke bisa kokarinsa na goyon bayan wannan gasar a karamar hukumar Demsa.
Alhaji Gambo Jika ya Kuma kirayi daluben da sukasance masu bin Ka idodin gasar a wani matakin ganin an samu nasaran gasar.
Gambo Jika ya kirayi iyaye da su lura da yaransu da Kuma kaisu makarantun addinin da na zamani domin samun inganceccen ilimi.
Shi ma a jawabinsa Hamman Batta Gladstone Alhamdu Teneke shikam kirayayi da a rungumin zaman lafiya da hadin Kai da oda Samar da zaman lafiya a tsakanin Al ummah.
Hamman Batta Wanda Hakimin Kawon Donwaya Alhaji Isah Zura ya wakikta ya yabawa wadanda suka shirya wannan gasar karo na 39 da za a gudanar a karamar hukumar Demsa,
A cewarsa masarautar Demsa a shirye take wajen bada hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran gudanar da gasar.
A sakonsu da suka gudanar Mallam Ali Mamman Shu aibu mashawarci na musamman akan harkokin addinin musulunci ga gwamna Fintiri, Mallam Sahabo Magani shugaban kungiyar Izala a jahar Adamawa dukkaninsu sun baiyana godiyarsu da fatan alherinsu dangane da shirya wannan musabaka musammanma a karamar hukumar Demsa.
Comments
Post a Comment