Hadin Kai a tsakanin Al umma abune da yake da muhimmanci..............Mallam Gambo Jika. Hamman Batta.
A kokarinta na Samar da hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma majalisar harkokin Addinin musulunci ta yabawa Hamman Batta Gladstone Alhamdu Teneke bisa kokarinsa na Samar da hadin Kai da zaman lafiya a karamar hukumar Demsa da ma jaha baki Daya.
Shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika ne ya baiyana haka a lokacinda ya jagoranci tawagan majalisar zuwa Kai ziyara a fadar Hamman Batta dake karamar hukumar Demsa a jahar Adamawa.
Mallam Gambo Jika yace sun kasance a fadar Hamman Battan ne domin su jinjina masa kan kokarin da yayi na daukar nauyin gasar karatun Al Qur ani Mai girma na wannan shekara dake gudana yanzu haka a karamar hukumar ta Demsa.
Mallam Gambo yace saboda haka suka ga ya dace su kawo masa ziyaran godiya ta summan, saboda haka majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa tana mika godiyarta da jinjinawarta ga Hamman Batta.
Ya Kuma kirayi basaraken da kada ya yarda da wasu wadanda ke kokarin rarraba kan Al umma domin acewarsa akwai wasu Banda kokarin tada fitina ba abinda sukeyi, saboda haka ayi taka tsantsan da irin wadannan mutane.
Ya Kuma yabawa masaraken bisa kokarinsa na Samar da zaman lafiya da hadin Kai a cikin karamar hukumar ta Demsa Wanda Kuma yin haka shi yake kawo cigaba a kowane bangare.
Shima a jawabinsa Hamman Batta Gladstone Alhamdu Teneke ya godewa majalisar addinin musulunci bisa wannan ziyar da ta kawo masa Kuma a shirye yake ya baiwa majalisar hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu cigaban zaman lafiya da Kuma hadin Kai a tsakanin Al umma.
Basaraken ya yabawa majalisar ta addinin musulunci a jahar Adamawa bisa kokarinta na kawo hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al ummar jahar ta Adamawa dama kewaye. Don haka su fadada aiyukansu zuwa lugu lungu da Sako Sako domin ganin sakonnin sun isa ga ko Ina.
Ya Kuma Yi adu ar ganin an kammala gasar karatun Al Qur ani karo na 39 da ke gudana a Demsa lafiya na tare da wasu matsaloliba.
A kashe ya shawarci Al umma da akasance tsintsiya ma daurinki Daya tare da taimakawa juna dama tausayawa juna da mutunta juna da Kuma nunawa juna kauna a Koda yaushe Wanda acewarsa haka zai bunkasa zaman lafiya da hadin Kai a tsakanin Al umma.
Comments
Post a Comment