Inganta tsaro an bukaci masu rike da masarautun gargajiya su bada tasu gudumawa wajen inganta tsaro a fadin jahar Adamawa.

 







Domin Samar da wadaceccen tsaro an bukaci masu rike da masarautun baka sukasance masu baiwa masarautun gargajiya hadin Kai da goyon baya domin magance matsalar tsaro a tsakanin Al ummah.





 Kauran Adamawa Mustafa Barkidindo Aliyu Mustafa ne ya baiyana haka a lokacin da yake jawabi a ziyaran godiya Wanda AbdulRahaman Ibrahim gobe  zantashi Kuma Sarkin bakan Adamawa ya Kai masa a Yola.





Mustafa Barkindo  yace masu rike da masarautun baka suna da rawa da zasu iya takawa wajen taimakawa bangaren tsaro, saboda haka akwai bukatar su zage damtse domin maida hankali a bangaren tsaro.




Ya shawarci Sarkin Bakan na Adamawa wato AbdulRahman Ibrahim da ya kasance Yana baiwa fadar maimartaba lamidon Adamawa hadin Kai da goyon baya domin ganin ya cimma burinsa na inganta tsaro da Kuma cigaban fadar.




Ya godewa Sarkin Bakan bisa ziyaran godiya da ya kawo masa Kuma shirye yake ta Bashi goyon baya da hadin Kai a Koda yaushe domin samun nasaran gudanar da aiyukansa yadda ya kamata.




A jawabinsa Hakimin riko na Jimeta Muhammed Cibado yace sun kasance a fadar ne  domin nuna godiyarsu dangane da sarautar Sarkin Baka  Adamawa da aka baiwa AbdulRahman Ibrahim. Wanda wannan abin farin cikine.




Ya Kuma jadddada mubaya arsu ga masarautar FOMBINA domin samun cigaban masarautar da ma hadin Kai a tsakanin masu rike da masarautun gargajiya da ke masarautar ta FOMBINA.




Shima da yake jawabi Sarkin Bakan Adamawa AbdulRahman Ibrahim Gobe zantashi ya baiyana farin cikinsa da jindadinsa tare da godiyarsa ga masarautar FOMBINA bisa wannan dama da masarautar ta Bashi Kuma a shirye yake ya baiwa masarautar hadin Kai da goyon baya domin cigaban masarautar.




Alhaji AbdulRahman Ibrahim ya kirayi sauran masu rike da masarautun gargajiya da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin cigaban masarautar harma da wanzar da zaman lafiya.




Sakin Bakan Adamawa na Adamawa dai ya Kai ziyaran ne tare da rakiyar Hakimin Jimeta Muhammed Chibado, Yan uwa da abokan Arziki harma da Yan jarida. da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE