Kungiyar NATAIS ta gudanar da taronta na kasa da kasa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

 











Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bukaci makamai dake karantar da harshen larabci da su fadada aiyukansu zuwa Yan kunan karkara domin bunkasa harshen larabci dama addinin musulunci domin Samar da cigaba harma da wanzar da zaman lafiya.





Gwamnan Fintiri ya baiyana haka ne a lokacinda yake jawabi a wurin taron kasa da kasa da kungiyar Makamai masu karantar da harshen larabci da addinin musulunci ta kasa wato NATAIS ta shirya tare da hadin gwiwar majakisar harkokin addinin musulunci jahar Adamawa da aka gudanar anan Yola.




Gwamnan Wanda maibashi shawara ta musamman akan harkokin asdini Mallam Ali Mamman Shu aibu ya wakikta yace Yana da matukan muhimmanci malamain su fadada aiyukansu zuwa Yan kunan karkara Wanda a cewarsa ana samun karanci malamain harshen larabci a yankunan karkara saboda haka Yana da kyau a bunkasa harshen larabci a yankunan karkara.




Gwamnan ya jaddada goyon bayansa ga kungiyar ta NATAIS domin ganin kungiyar ta samu damar gudanar da aiyukanta yadda ya kamata.




Ya Kuma yabawa kungiyar bisa zabar jahar Adamawa domin gudanar da taron kungiyar Karo na 41 a jahar Adamawa.





Shima a jawabinsa shugaban majakisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika ya godewa  kungiyar ta NATAIS tare da tabbatar da cewa majakisar addinin musulunci a shirye take ta baiwa kungiyar ta NATAIS hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na bunkasa harshen larabci.




Malam Gambo ya shawarci Al ummah musulmai da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaba addinin musulunci yadda ya kamata.




Da yake nashi jawabi shugaban kungiyar NATAIS din na kasa Farfesa Musa Adesina AbdulRaheem ya baiyana dalilinsu na shiraya wannan taro da zumar Samar da hadin Kai da zaman lafiya Wanda ma taken taron shine zaman lafiya da tsaro.




Ya yabawa gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri bisa goyon bayan da ya baiwa kungiyar ya Kuma Yi masa adu ar Allah madaukakin sarki ya Bashi nasaran cigaba da aiyukan cigaban jahar.




Shima da yake gabatar da jawabinsa Farfesa Umar A Pate ya shawarci Yan Najeriya da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Al umma da Kuma Samar hadin Kai a tsakanin Al umma.





Shi kuwa Mai Alfarma Sarkin musulmai Alhaji Muhammadu Sa ad Abubakar III Wanda Alhaji Shafi u Abdullahi wakikin Makarantar Zazzau ya wakikta ya yabawa kungiyar bisa Shirya wannan taro Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban harshen larabci.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE