Manoma da makiyaya an bukacesu da su rungumin zaman lafiya a tsakaninsu.
A wani mataki na kawo kashen ta kaddama a tsakanin makiyaya da manoma fadin Najeriya an shawarcesu da sukasance masu hada kansu da fahintar juna a tsakaninsu domin wanzar da zaman lafiya Mai daurewa da Kuma cigaban aiyukansu yadda ya kamata.
Kwamnadan Mafarauta na kasa Kuma Sarkin yakin mafarauta Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola.
Alhaji Muhammed Adamu yace ya kamata manoma da makiyaya su sani cewa su Yan uwan junanne kar su bari shaidan ya shiga tsakaninsu, sukasance masu taimakawa juna da yarda da juna a Koda yaushe domin ganin ba a samu tashin hankali a tsakaninsuba.
Alhaji Adamu yace rikici a tsakanin manoma da makiyaya ba karamin koma baya bane musammanma a bangaren tattalin arziki da asaran rayuka dama dukiyoyi masu yawa.
Acewarsa dai ya kamata manoma da makiyaya su kaucewa duk abinda zai kawo tashin taahina a tsakaninsu su rungumi zaman lafiya da taimakawa juna domin samun cigaba.
Ya Kuma shawarcesu da su daina daukan doka a hannunau duk abinda suka gani ba daidaiba to su sanar da hukumomin tsaro domin daukan matakinda suka dace dangane da lamarin.
Ya Kuma bukaci manoma da makiyaya da sukasance masu kiyaye hakkin juna a Koda yaushe wand a cewarsa hakan zaitaimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Harwayau Alhaji Muhammed Adamu ya kirayi gwamnatoci dama masu ruwa da tsaki da sukasance masu shiga tsakanin manoma da makiyaya a Koda yaushe tare da musu iyaka ta hanyar ware wa kowa iyakarsa musammanma ware wuraren kiwo ga makiyaya a fadin Najeriya Wanda hakan zai kawo kashen tada jijiyar wuya a tsakanin manoma da makiyaya.
Alhaji Muhammed Adamu yayi Adu ar Allah madaukakin sarki ya wanzar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya, da Kuma kawo karshen duk wani kalubalen tsaro a fadin Najeriya.
Rikici a tsakanin manoma da makiyaya dai ya Dade Yan ciwa gwamnatin dama jama a tuwo a kwarya lamarin da ke sanadiyar asarar rayuka dama dukiyoyi masu yawa tare da kona gidaje da dai sauransu.
Comments
Post a Comment