Matsalar tsaro: An bukaci Al umma da sukasance masu yin adu o I a Koda yaushe.
An kirayi Al umma musulmai da sukasance masu maida hankali wajen yin adu o I a Koda yaushe domin neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar rayuwa da ake ciki dama kalunaken tsaro da kasar nan ke fuskantar.
Babban Limamin Masallacin Jumma a dake barikin Yan sanda a Yola CSP Ahmed Suleiman ne yayi wannan kira a hudubarsa na Jumma da ya gabatar a Masallacin.
CSP Ahmed Suleiman yace Adu ar abune da take da matukan muhimmanci a rayuwar Al umma musulmai don haka bai kamata Al umma musulmai sukasance masu yin sakaci da yin adu a ba.
A cewarsa Babban Limamin Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbatar a gareshi ya baiyana cewa adu a itace takwabin mumini saboda haka Al umma musulmai su zage damtee wajen yin adu a I da Kuma kaucewa sabawa Allah madaukakin sarki domin Samar da zaman lafiya a mai daurewa.
CSP Ahmed ya Kuma shawarci iyaye da sukasance masu yiwa yaransu adu o I fatan Alheri su daina la antar yaransu sukasance masu maida hankali wajen Yi musu adu o I domin inganta rayuwarsu.
CSP ya Kuma kirayi Al umma musulmai da sukasance suna yiwa juna adu o I Alheri dama taimakawa juna a Koda yaushe domin samun hadin Kai dama cigaban addinin musulumci.
Ya Kuma Kara da cewa Al umma musulmai sukasance masu yiwa kasa da shuwagabanin adu o I domin su samu damar yiwa Al umma adalci da Kuma aiyukan cigaba.
Comments
Post a Comment