OFAB ta karrama Alhaji Usman Abubakar a kasar Kenya.
Alhaji Usman Abubakar Wanda akafi sani da Manu Ngurore ya karbi lambar yabo da karramawa da hukumar inganta fasahar tsirai dake Afirka wato OFAB tayi masa akan kwarewarsa na harkokin noma a Afirka, a Mambasa kasar Kenya.
Alhaji Usman Abubakar ya karbi kautar yabon ne bayan kammala taron karawa juna sani na kwana Daya Wanda hukumar ta OFAB ta shirya a Mambasa a kasar Kenya.
Da yake gabatar da Lamar yabon Darektan hukumar ta OFAB a Afirka Dr Canisius Kanangire yace dalilin baiwa Alhaji Usman Abubakar lambar yabon dai shine irin gudumawar da ya bayar kan cigaban harkokin noma a Afirka.
An Kuma shawarceshi da ya cigaba da irin wannan taimako da yakeyi ga manoma domin ganin an samu wadaceccen abunci a yankin kasashen Afirka.
Da yake karban lambar yabon Alhaji Usman Abubakar ya godewa hukumar ta OFAB bisa bashin wannan lambar yabo tare da yin alkawarin cigaba da kokarin da bada gudumawa a bangaren noma domin magance kalubalen da ake samu a harkokin noma a yankin Afirka.
Ya Kuma yabawa Dr Canisius Kanangire bisa gurmanawa da suka yi masa Kuma zaiyi dukkanin maiyiwa domin cigaban harkokin noma a yankin Afirka.
Comments
Post a Comment