Wasu matasa sun shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa.

 






Rundunan Yan sanda a jahar Adamawa tayi nasaran cafke wasu matasa hudu da ake zargi da aikata laifuka ciki harda yiwa wata yarinya yar shekaru17 fyade .




Matasan dai wadanda shekarunsu ya kama daga 16 zuwa 17 dukkaninsu daluben ne a Makarantar sakandaren gwamnati dake Sugu a karamar hukumar Ganye dake jahar Adamawa.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Sanarwan ta baiyana cewa tunin kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris  ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da lamarin domin daukan matakin da ya dace.




A cewar sanarwan dai an samu nasaran kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafi da wata Mai Suna Veronica Kezitto mazauniyar Garin na Sugu kan cewa akwai wasu da suka yiwa wata yarinya yar shekaru 17 da haifuwa fyade bayan sun shayar da ita da giya.




A yayin gudanar da binciken wadanda ake zargin sun amsa lafukansu tare da yiwa doka Karan tsaye.



Kwamishinan ya Yan sandan jahar ta Adamawa ya baiyana takaicinsa dangane da aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa za abi dokan da ta dace wajen gudanar da bincike.



Kwamishinan ya Kuma gargadi Jama a musammanma iyaye da sukasance masu maida hankali a kan yaransu a Koda yaushe tare Kuma da gaggauta Kai rahoton abinda basu anince da Shiba akan lokacin ga ofishin Yan sanda.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE