ZAMAN LAFIYA: An bukaci Mafarauta su hada kansu a matsayin tsintsiya madaurinki Daya.

 











A kokarinta na taimakawa hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a fadin Najeriya an kirayi kungiyar Mafarauta da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaban kungiyar a fadin Najeriya.




Kwamandan Mafarauta na kasa Kuma Sarkin yakin Mafarautar Adamawa Alhaji Muhammed Adamu ne yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.





Alhaji Muhammed Adamu yace hadin Kai a tsakanin membobin kungiyar Yana da matukan muhimmanci saboda hadin Kai dinne zai kawo cigaban kungiyar ya Kuma shawarcesu da sukance masu rikon amana da yarda da juna da gudanar da aiyuka bisa tsaron Allah wand a cewarsa hakan zai kawo zaman lafiya da cigaba a cikin kungiyar.






A cewarsa duk aiyukan  kungiyar abu dayane saboda haka bai dalilinda yasa ake samu rarrabuwar Kai ba, saboda haka ya kamata sukasance masu hada kansu domin ganin sun cimma burinsa na taimakawa hukumomin tsaro a fadin Najeriya.




Ya Kuma baiyana cewa Mafarauta suna bada muhimmiyar gudumawa wajen taimakawa hukumomin tsaro da suka hada da aojoji, Yan sanda, civil Defence, da dai sauransu.





Alhaji Adamu ya jaddada aniyar kungiyar ta Mafarauta a shirye take ta cigaba da taimakawa hukumomin tsaro domin Kara musu kwarin gwiwar dakile kalubalen tsaro a fadin Najeriya.





Saboda haka mafarautan sukasance tsintsiya ma daurinki Daya da Kuma hakuri da juna a kodayaushe domin samun cigaban kungiyar yadda ya kamata.




Ya Kuma shawarci Al umma da sukasance suna baiwa mafarautar hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu damar gudanar da aiyukanta yadda yakamat domin kare rayuka da Kuma dukiyoyin Jamma a.




Ya Kara da shawartan Yan Najeriya da su cigaba da yin adu o I domin Neman taimakon Allah wajen kawo karshen kalubalen tsaro dake ciwa gwamnati tuwo a kwarya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE