An bukaci gwamnatin jahar Adamawa da ta shiryawa matasa bita dangane da illar shaye shaye a tsakanin matasa.

 









An kirayi gwamnatin jahar Adamawa da tayi dukkanin abinda suka dace domin magance matsalar shaye shaye a tsakanin matasa a wani mataki na inganta rayuwar matasa a fadin jahar.





Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheirk Abdullahi Bala Lau ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin bikin yaye daluben mahaddata Al kur ani maigirma Wanda Makarantar NA IBI ta shirya a Yola.





Sheirk Abdullahi Bala Lau yace Yana da muhimmanci gwamnatin jahar Adamawa ta dauki matakin shiryawa matasa bita na musamman domin wayar musu da Kai dangane da illar ta ammala da muyagun kwayoyi tare da sauya musu tunani ta hanyar koyar dasu sana o I daban daban.




Sheirk Abdullahi Bala Lau ya baiyana cewa Jan matasan ajiki da Kuma wayar musu da Kai zaitaimaka wajen dakile matsalar shaye shayen a tsakanin matasa Wanda Kuma hakan zai basu damar inganta rayuwarsu yadda ya kamata.





Sheirk Abdullahi Bala Lau ya shawarci dukkanin masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya, shuwagabanin addinai, shuwagabanin Al umma da suma su bada tasu gudumawa domin kawar da matsalar ta ammali da muyagun kwayoyi a tsakanin matasa dake fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE