An bukaci manoma da su rungumi noma Auduga a zamunance.

 










Domin ganin an bunkasa harkokin noman Auduga a jahar Adamawa dama Najeriya an shawarci manoma da su rungumi noman Auduga domin cigaban yadda ya kamata.





Mashawarci na musamman akan harkokin noma da sana a ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Alhaji Usman Abubakar Wanda aka fi sani da Manu Ngurore ne ya bada wannan shawara a lokacinda yake jawabi a wurin taron gangamin wayarwa manoma Kai dangane da bunkasa harkokin noma Auduga a Ngorore dake jahar Adamawa.







Alhaji Usman Abubakar yace tun a shekara ta 2016 ne dai aka fara shigo da irin Auduga da Ka ingantaahi a kimiyance wato BTcotton domin baiwa manoman Auduga damar bunkasa aiyukansu, yadda ya kamata.











Alhaji Manu Ngurore ya baiyana cewa yin amfani da irin Auduga da aka inganta fasaharsa Yana bada yabaiya Mai yawa fiye da Wanda ba a inganta fasaharsaba. A cewarsa indan mutum ya noma kadada Daya na irin da aka ingantaahi to zai samu yawan Auduga da ya Kai ton uku da rabi a yayin da Wanda ba a ingantaahi shikam ton Daya zai bayar.





Alhaji Usman yace tun da farko dai anyi gwajin irin da manoma Dari biyar a fadin Najeriya Wanda Kuma an samu nasaran sosai don duk wadanda suka gwada a gonakainsu sun samu yabaiyya Mai kyau Wanda hakan ya baiwa manoma damar cigaba da noma audugan.




Alhaji Usman Abubakar ya kirayi manoma da sukasance suna amfani da irin Auduga da aka inganta fasaharsa a gonakainsu domin bunkasa harkokin noman Auduga tare da inganta tattalin arziki harma da Samar da aikinyi a wani mataki na rage rashin aikinyi a tsakanin matasa.











Ya Kuma kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai da Yan majalisar dokokin kasa harma da masu ruwa da tsaki da su baiwa tsarin hadin Kai da goyon baya domin samun damar bunkasa noman Auduga a Najeriya. Wanda Kuma hakan zaitaimakawa matasa rungumar noman Auduga.





Harwayau ya baiyana cewa Shima ya dauki tsawon lokaci Yana noma Auduga Wanda hakan yasa ya samu lambar yabo a kasa Kenya tare Kuma da halartan taron inda ya wakilci arewacin Najeriya Wanda akayi  kan harkokin noman Auduga a jahuriyar Benin.




Saboda haka manoma karsuyi da wasa wajen rungumar tare da maida hankali wajen noma Auduga domin zasu samu cigaba yadda ya kamata.






Da yake nashi jawabi Jami in hukumar inganta fasahar irin na Auduga daga kasar Indiya Mr Rabith yace sun kawo irin wannan irin ne domin ganin manoma Auduga a Najeriya sun amfana domin bunkasa harkokin noman Auduga.





Ya Kuma kirayi manoman da su maida hankali wajen noma irin wannan irin Auduga da aka inganta fasaharsa domin ganin basuyi asaraba.





A cewarsa yin amfani da irin Auduga da aka inganta fasaharsa Yana da muhimmanci tare da Samar da kudade masu yawa.




Saboda haka Shima ya jaddada kiransa ga monoman da su fadada aiyukansu wajen noma Auduga Wanda acewarsa ba zasuyi asaraba Kuma zasu samu kasuwar Mai kyau.





Wasu daga cikin manoman da suka shuka irin Auduga da aka ingantaahi sun baiyana Jin dadinsu da fara cikinsu dangane da noma irin audugan inda sukace sun samu yabaiya Mai yawa dama Auduga. Saboda haka sukam zasu cigaba da noma irin Auduga da aka inganta fasaharsa domin samun cigaba harma da bunkasa tattalin arzikin jahar dama kasa baki Daya.




Taron dai ya samu halartan masu ruwa da tsaki dama sarakunan gargajiya daga sassa daban daban.


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE