Anyi bikin bude makarantar RAYATUl HUDA.dake bayan ofishin Yan sanda jimeta a karamar hukumar Yola ta arewa.
An baiyana cewa Neman ilimi abune da yake da muhimmanci a rayuwa domin shine silar duk wani cigaba. Al umma baki Daya.
Malam malami Garba ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi a wurin bikin bude Makarantar RAYATIK HUDA Wanda take bayan ofishon Yan sandan Jimeta Wanda ya gudanar a harabar Makarantar dake Yola.
Malam malami Garba ya zanyano irin muhimmanci da ilimi ke dashi da suka hada zaman lafiya, hadin Kai, cigaba da dai sauransu.
Don haka nema yace Yana da kyau Al umma musulmai su maida hankali wajen Neman ilimi wa kansu da iyalensu kamar yadda mazon Allah madaukakin sarki yace nema ilimi wajibine.
Saboda haka ya shawarci Al umma musulmai su dukufa wajen fadada koyar da ilimi a lunguna da Sako Sako harm da maida hankali wajen tura yara makarantu domin a cewarsa hakan zai bunkasa ilimi a tsakanin Al umma yadda ya kamata.
Shima a jawabinsa Malam Umar Zingina shikam kira yayiwa Al umma musulmai da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin ganin an samu cigaba bunkasa addinin musulunci yadda ya kamata.
Malam Zingina ya baiyana cewa Allah madaukakin sarki a cikin Al Qur ani Mai girma yace Al umma musulmai sukasance Yan uwan juna kada su rarraba.
Saboda Yana da matukan muhimmanci Al umma musulmai sukasance sunayin dukkanin abinda zaikawo hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
Shima ya kirayi iyaye da sukasance suna tura yaransu makarantu addini Dana zamani Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen fadada ilimi da hadin Kai.
Malam Mukhtar Dayyib Wanda shinema shugaban Makarantar RAYATUL HUDA an bude Makarantar ne da zumar bada ilimi ga yaran a fannoni daban daban da suka hada Dana addini harma Dana zamani.
Don haka nema yake kira ga iyaye a duk inda suke sukasance sun kawo yaransu Makarantar domin a cewarsa marantar ta kimtsa tsaf domin baiwa yara inganceccen ilimi a bagarori daban daban domin Samar da cigaban addinin yadda ya kamata.
Mallam Mukhtar Dayyib ya baiyana cewa Makarantar tana da kwarararrun makamai a fannoni daban daban don haka iyaye karsuyi shakka kawo yaransu ba tare da Bata lokaciba.
Ya Kuma kirayi masu hanu da shuni da sukasance suna tallafawa Makarantar da kudadensu koma da ahawarwari domin ganin Makarantar ta cimma burinta na bunkasa ilimi a tsakanin yara.
Da yake nashi jawabi wakikin makamai jahar Adamawa Ustas Safiyanu Liman iya runde ya yabawa jagororin Makarantar bisa na mijijn kokari da sukayi domin Samar da Makarantar Wanda a cewarsa hakan zai kawo cigaba sosai.
Shima anashi bangaren Hakimin Jimeta Muhammed Cibado ya yaba da yadda aka bude Makaranta tare da bada shawara ga iyaye da sukasance sun turo yaransu Makarantar domin su samu inganceccen ilimi.
Hakimin ya Kuma shawarci Al umma musulmai da sukasance sun baiwa lokaci muhimmanci tare Kuma da Kara himma wajen Neman ilimi a Koda yaushe domin Samar da zaman lafiya da cigaba.
Comments
Post a Comment