Kungiyar IMWON ta shirya taron karawa juna sani a jahar Adamawa. tare da karrama membobinta.
An shawarci kungiyar mata musulmai dake taimakawa marayu da marassa galihu a Najeriya IMWON shiyar jahar Adamawa da ta fadada Da awarta zuwa karkara, dama Sako Sako domin ganin ta cimma nasaran aiyukanta yadda yakamata.
Malam Isma ila Ishaku ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake gabatar da lakca a wajen taron karawa juna sani Wanda kungiyar ta IMWON karkashin jagoranci Hajiya Asma u Abubakar ta shirya a Yola.
Malam Isma ila yace aikin Da awa aikine da yake cike da kalu bale don haka ya kamata sukasance masu hakuri da Kuma juriya a lokacinda suke gudanar da aiyukan Da awa. Ya Kuma bukacesu da su fadada aikin Da wa zuwa kyauyuka domin acewarsa akwai Jan aiki don haryanzu akwai wasu da basu fahinci dokokin addininba.
Malam Isma ila ya shawarcesu su Kara azama wajen shirya bitici akai akai Wanda hakan zai taimaka duk dacewa abune da yake da bukatar kudi don haka nema ya kirayesu wajen rungumar sana o I dama koyar da sana o I domin samun nasaran abinda suka sanya agaba.
Daga bisani dai an baiwa wasu membobin kungiyar kwambu yabo biyo bayan rawa da suka taka wajen cigaban kungiyar.
Kungiyar ta IMWON dai ta karrama Amiran kungiyar shiyar karamar hukumar Ganye wato Bilkisu, sauran sun hada da Hajiya Aisha Abubakar Mahmud maman IMWON a karamar hukumar Ganye .
An dai gabatar da jawabinsa daban daban. a wurin taron inda aka bukaci kungiyar ta kasance masu hada kansu da Kuma yin aiki tukuru domin ganin an samu hadin Kai a tsakanin Al umma musulmai.
An Kuma yaba wa kungiyar ta IMWON bisa kokari da takeyi wajen shirya irin wannan bita tare da kirata da ta cigaba da irin wannan aiki domin samun zaman lafiya Mai daurewa.
.Da take nata jawabi Amiran Kungiyar a jahar Adamawa Hajiya Asma u Abubakar tace Yana daga cikin aiyukan kungiyar na shirya irin wannan bita Kuma kungiyar da gabatar da aiyukan Da awa a wurare daban daban ciki da wajen jahar Adamawa.
Ya Kuma tabbatar da cewa zasuyi iya kokarinsu domin ganin sun cimma burinsu na aiyukan Da awa tare da Kiran Al umma da sukasance masu basu hadin Kai da goyon baya a wani matakin ganin sun samu nasaran.
Taron dai ya samu halartan Amiririn kananan hukumomin da ma membobin kungiyar dake ciki da wajen fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment