Rundunan tsaron Civil defence ta tura Jami anta 1600 a fadin jahar Adamawa a yayinda aka fuskanci bukukuwa.

 










A yayinda aka tinkari bukukuwar kirisimeti da sabuwar shekara hukumar tsaro bada kariya ga fararen hula a Najeriya wato Civil defence NSCDC shiyar jahar Adamawa ta kimtsa tsaf domin daukan matakan tsaro a wani mataki na bada kariya a lokacin dama bayan bukukuwar kirisimeti da sabuwar shekara a fadin jahar Adamawa baki Daya.





Rundunan ta Civil defence a shirye take ta kare kaddadorin kasa harma da wuraren taron jama a irinsu kasuwanni, wuraren taruruka,  harma da wuraren ibadu domin ganin an gudanar da bukukuwar cikin tsanaki.





Kakakin rundunan ta NSCDC a jahar Adamawa DSC Amidu Nyako Baba ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.






Sanarwan tace Rundunan karkashin jagoranci Kwamandan Idris D Bande ta tura Jami anta a dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar domin Samar da yanayi Mai kyau domin baiwa Al umma damar gudanar da bukukuwarsu lafiya ba tare da fargaba ba.





Sanarwan ta Kara da cewa rundunan ta NSCDC tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro saboda inganta tsaro yadda ya kamata.




Kwamandan rundunan Idris Bande ya tabbatarwa Al ummar cewa rundunan zata baiwa Al umma kariya kafin, lokaci, dama bayan bukukuwar da ke tafai. Tare da Kiran daukacin Al umma da su taimakawa rundunan da wasu bayanai dama sanya ido domin daukan matakin gaggawa wajen dakile matsaloli da kan iya tasowa.




Rundunan ta kudiri aniyar ganin anbi doka da oda a lokacin bukukuwar a fadin jahar ta Adamawa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE