Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta cika hanu da mutane uku da ake zargi da safaran muyagun kwayoyi.
A kokarinta na dakile aikata laifuka dangane da safaran muyagun kwayoyi rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane uku tare da gano muyagun kwayoyi a wurin wadanda ake zargi .
Rundunan tayi nasaran kama wadanda ake zarginne biyo bayan bayanain sirri Wanda hakan yasa aka Kai samame a maboyar muyagun a Malabu dake cikin karamar hukumar Fufore a jahar Adamawa.
Kakakin rundunan Yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace biyo bayan samamen ne rundunan ta samu nasaran kama mutane uku da ake zargi harma da gano tabar wiwi, da kwayoyi masu hatsari, da dai sauransu a wurin wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargindai sun hada da Shafi u Musa, Idris Muhammed, Bashiru Nasiru, dukkaninsu mazauna garin na Malabu ne Kuma sun amsa kaifinsu na aikata sarafa muyagun kwayoyin.
Sanarwan ta Kara da cewa rundunan tana kan bakanta na inganta tsaro a fadin jahar domin tabbatar da tsaro a tsakanin Al ummar dake fadin jahar.
Comments
Post a Comment