Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta baza komarta domin farauto wadanda sukayi garkuwa da fastocin guda biyu a karamar hukumar Fufore dake jahar Adamawa.










Rundunan Yan sandan a jahar Adamawa ta nuna alhininta da Jin dadinta dangane da garkuwa da akayiwa fastocin da suka da pastor Ishaku D Chiwar da Reverend James Kwayam na mujami ar EYN dake Billa Malabu lamarin yafaru da sanyar safiyar yau 30-12-2024.





Kakakin rundunan yam sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



Lamarin ya faru a garin Blla Malabu dake cikin karamar hukumar Fofore , inda masu garkuwa da mutane suka tinkari Gidan fastocin dake Hayin gada Wanda hakan yasa sukayi garkuwa da fastocin.





Masu garkuwa da mutanen dai sunyi amfani da makamai masu karfi a Gidan fastocin da misalin karfe 2:00 na dare, kafin suyi awun gaba da su.




Da faruwa lamarin hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya bada umurnin tura Jami an yan sanda domin farauto masu garkuwa da mutanen a maboyarsu da Kuma ceto mutanen biyu.




Rundunan zaragi dukkanin kokari bankado duk Wanda yake da hanu a lamarin tare da yin adalci, kwamishinan ya tabbatar da cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin Al umma daga duk wani tashin hankali, a fadin jahar.




Kwamishinan yace rundunan nazata lamunce da garkuwa da akayiwa shuwagabannin addinainba saboda suna aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki domin inganta tsaro.




Rundunan yan sandan ta  kirayi Al umma da sukasance suna baiwa rundunan hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma nasaran kare rayuka dama dukiyoyin Al umma baki Daya.



Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE