Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama mutane sama da Dari bakwai tare da yankewa mutane sama da Dari biyu hukunci a shekaran 2024.
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran cafke mutane sama da Dari bakwai da Sha biyar saboda aikata laifuka daban daban da suka hada da yin garkuwa da mutane, Fashi da makamai, aikin Shila, yin fyade, kisan Kai harma da rikici a tsakanin manoma da makiyaya da dai sauransu.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ne ya baiyana haka a lokacinda yake yiwa manema labarai jawabi dangane da nasarori da rundunan tayi a shekara ta 2024.
Kwamishinan yace tunda ya fara aiki daga watan febuwarin shekara ta 2024 rundunan tayi nasaran gudanar da aiyukanta harma da yaki da aikata laifuka a fadin jahar baki Daya.
Kwamishinan ya baiyana cewa rundunan ta samu nasaran ne ta yadda suke Kai samame a wurare daban daban ciki harda maboyar masu aikata laifi da Kuma kiraye kiraye da ake musu da dai sauransu.
Kwamishinan yace a shekara da 2024 rundunan ta samu laifuka 315 tare da ceto mutane 21 ba tare da rauniba, ta Kuma gano arbarushe 432 da bindigogi 17 da motoci da dai sauransu a fadin jahar.
Dankwambo Morris ya Kara da cewa an yankewa mutane 292 hukunci a yayinda mutane 387 suna jiran shariya ana Kuma cigaba da binciken mutane shida.
Harwayau kwamishinan Yan sandan yace rundunan bazatayi kasa a gwiwaba wajen cigaba da yaki da aikata laifuka a shekara ta 2025 don haka Yana bukatan daukacin Al ummar jahar Adamawa sucigaba da taimakawa rundunan Yan sandan da wasu bayanai da zasu taimaka wajen yin nasaran dakile aikata laifuka.
Yace Jami an Yan sandan zasu kasance suna gudanar da aiyukansu bisa kwarewa da bin doka domin kare rayuka da dukiyoyin Al umma, ya Kuma tabbatar da cewa za a dauki kwararan matakan tsaro domin ganin an gudanar da bukukuwar kirisimeti Dana sabuwar shekara lafiya.
Kwamishinan Yan sandan ya gargadi jama a da sukaucewa yin amfani da knock out domin rundunan bazata lamunvewa duk Mai karya dokaba.
Ya Kuma godewa tare da yabawa gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na baiwa rundunan goyon baya na ganin an kawo karshen aikata laifuka a fadin jahar.
Ya godewa Yan jarida bisa na mijijn kokari da sukeyi wajen bada gudumawa domin dakile aikata laifuka.
Anashi bangaren mashawarci na musamman akan tsaro da zaman lafiya ga gwamna Ahmadu Fintiri. Ahmed Lawan ya yabawa rundunan Yan sandan bisa kokarinsu na dakile batun matsalar tsaro a fadin jahar.
Ahmed Lawan yace gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zata cigaba da baiwa rundunan Yan sandan goyon baya domin ta samu nasaran kare rayuka dama dukiyoyin Al umma a fadin jahar.
Comments
Post a Comment