Akalla Yan sanda Dari da goma ne suka samu Karin girma daban daban a jahar Adamawa.








A ranan talata rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta karawa jamin anta 110 Karin girma zuwa mukamai na gaba Wanda Kuma kwamishin Yan sandan jahar ta Adamawa Dankwambo Morris ya jagoranta, Wanda ya gudanar cikin taron jama a harma da Yan uwa da abokan Arziki Wanda sukazo domin tayasu murnan.





Kakakin rundunan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa mama labarai a Yola.





Sha biyar daga cikinsu dai an Kara musu matsayin daga safirintandan dan sanda wato SP zuwa Babban Safiritanda wato CSP, wadanda suka hada da Alfired Future DPO Numan, Aliyu Minda DPO Song, Inuwa Umar Alkali DPO Maiha, Muhammed Yahaya Nuhu, DPO Ganye, Musa Dansoho, DPO Gombi, Iliya Dauda DPO Dumne, Isa Jibrin, DPO Daware, Sale Ahmed DPO Shelleng da Kuma Abdulrauf Balarabe Suleiman DPO Kofare. Sauran sun hada da Jamilu Aliko Maishanu, Kwamandan Scorpion, Kwaji Hassan Mai kula da sashin Samar da kayakin, Abana Bamanga na sashin shariya, Adam Abdulmuttalif Mai kula da sashin provost, Umar  Ibrahim 2ic na sashin tattara bayanain sirri a jahar SID, Anuwa K Madaki 2ic na sashin yaki da Yan ta adda.




Sai Kuma Sha Daya daga cikinsu sun samu mukamin safiri tanda SP  daga mukamin mataimakan Safiritanda DSP Cikinsu akwai Andulmajeed Dahiru DPO Magulvu Mahadi, Mahdi Abubakar DPO Kiri, Musa Abubakar DPO Maraba, Adamu Saidu DPO Kabbi Lamba da Adamu Abubakar DOO Kala a sauran sun hada da Richard Yusuf 2ic CFO, Daniel Kindame kwamandan operation Farauta Philp Pakshida da Etim Shedrack. 




A yayinda 84 sukam sun samu Karin girma daga ASP zuwa DSP taron bikin dai Yana da matukan muhimmanci da Jami an wand ya nuna irin jajircewa da suke dashi.



A jawabinsa kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya Yaya wadanda suka samu Karin girma murna ind ya jaddada muhimmanci jajircewa bakin aiki inda ake tsammanin zasu Kara himma wajen gudanar da aiyukansu, ya shawarcesu da su dubi girma da suka samu tare da kiransu da su runaiya aiyukansu domin ganin jahar Adamawa ta samu kariya yadda ya kamata.




Shima anashi jawabi a madadin Wanda suka samu Karin girma  DPO Numan Alfred Future ya baiyana farin cikinsu tare da godewa Babban sifeton Yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun da hukumar kula da aiyukan Yan sanda tare Kuma da tawagan gudanarwan rundunan bisa Kara musu wannan girma domin a cewarsa wannan babbar damace a garesu tare da tabbatar da cewa zasu cigaba da gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin samun cigaban rundunan tare da yin biyayya dama girmamawa domin inganta tsaro a fadin jahar.






Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE