An kaddamar da fara bitan ga maniyatan karamar hukumar Yola ta Arewa a wani mataki na shirye shirye aikin hajjin shekara ta 2025.
Hukumar aikin hajji karamar hukumar Yola ta Arewa dake jahar Adamawa ta kaddamar da fara bita wa maniyatan karamar hukumar domin ganin maniyatan sun samu damar gudanar da aikin hajji shekara da 2025 lafiya na tare da matsalaba.
An dai kaddamar fara bitan ne a sakatariyar ofishin hukumar jun dadin alhazai na na jahar Adamawa dake Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Da yake jawabi dangane da aikin hajji a shari ance Malam Muhammed Chibado wandana shine zai jagogaranci bitan yace aikin hajji wajibine ga Wanda yake da iko sau Daya a rayuwa saboda haka da zaran mutum ya samu iko ya hanzarta zuwa aikin hajji domin a cewarsa aiki hajji aiki ne da yake da lada Mai yawa.
Ya ja hankalin maniyatan da sukasance masu maida hankali wajen aikin hajji yadda ya kamata domin fahintar yadda ake gudanar da aikin hajji harma da sanin Ka idodin aikin.
Shima anashi jawabi Malam Musa Usman ya shawarci maniyatan da sukasance masu halartan bitan akan lokaci Kuma ko da yaushe domin samun ilimin aikin hajji yadda ya kamata.
Ya Kuma tabbatar da cewa dukkanin Mai halartan bita zai samu Karin fahintar yadda zai gudanar da aikin hajji yadda ya kamata.
Shima a nashi jawabi Jami in tsare tsaren aikin hajjin karamar hukumar Yola ta Arewa Alhaji Ya u Gambo shinema shugaban Jami an aikin hajjin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa ya baiyana cewa an kaddamar da fara bitan akan lokacine domin basu damar gudanar da shirye shirye aikin hajjin cikin tsanaki.
Saboda haka nema Alhaji Ya u Gambo ya kirayi maniyatan da sukasance masu halartan bitan a Koda yaushe da Kuma maida hankali akan bitan sosai domin sanin yadda aikin hajji yake da Kuma sanin Ka idodin aikin.
Kwamired Suleiman Yusuf Uban doman Gulak Jami in tsare tsaren aikin hajjin Madagali Shima Jan hankalin maniyatan yayi da su kasance masu Kara azama wajen halartan bitan Wanda hakan zai bada damar yin aikin hajji ba tare da wani matsalaba.
Ya shawarci maniyatan da su matsa kaimi wajen baiyana kudaden ajiya Wanda hukumar aikin hajjin kasa ta aiyana Wanda Kuma za arufe a karshen wannan wata da muke ciki.
Taron bitan ya samu halartan makamai da dama ciki harda Jami in tsare tsaren aikin hajjin karamar hukumar Girei Alhaji Salihu Garba.
Comments
Post a Comment