Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar da sabon farashin kujerar aikin Hajjin bana.











Yayin wata hira da ya yi da BBC, shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce kujerar aikin hajjin kamar yaushe ta kasu kashi uku inda wadanda za su je Hajjin daga kudancin Najeriya kudinsu ya fi na wadanda zasu tashi daga arewa maso gabas da na arewa masau yammacin Najeriya.



Ya ce," Ga alhazan da za su tashi daga jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya kamar Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi, za su biya kudin da ya kai naira miliyan 8,457,685.59.Sai kuma wadanda za su tashi daga arewa maso gabashin Najeriya wadanda su sun fi kusa da Makka, wato wadanda suka fio daga jihohin Adamawa da Yobe da Borno da Gombe da Bauchi da kuma Taraba za su biya naira miliyan 8,327,127.59."

"Wadanda za su tashi daga jihohin kudancin Najeriya kuma za su biya naira miliyan 8,784,85.59." in ji shi.


Shugaban hukumar na NAHCON, ya ce kudin kujerar aikin hajjin ta bana da kadan ya dara na bara.

Ya ce, " Da farko mun tsorata domin muna ganin kudin kujerar bana zai iya kai wa naira miliyan 10 koma fiye da haka, to amma da taimakon Allah da kuma tuntuba da bibiyar wadanda ke yi wa alhazai hidima a can Saudiya da muka yi shi ya sa aka samu sauki."

Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ya ce "Mun yi kokari mun samu sauki a kan kudaden da ake kashewa alhazai a Mina da wajen Arfah da Muzdalifa saboda tattaunawar da muka yi da wadanda abin ya shafa a can."

Shugaban hukumar alhazan na Najeriya, ya ce a cikin wannan kudin kujera babu tallafin gwamnati ko kadan.

"Dangane da batun kudin guzurin alhazai kuwa a bana ma dala dari biyar za a bawa kowane alhaji kamar bara."

Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya ce, sun yi gyare-gyare sosai domin gudun fuskantar matsalar da aka samu a hajjin bara musamman a zaman Mina kan batun tantunan manyan baki.

Kazalika ya sanar da ranar karshe ta biyan kudin kujerar aikin hajjin bana 2025, inda ya ce "Duk maniyyacin da bai biya kudinsa har zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2025, to gara ma ya hakura ya bari sai badi.

Ya ce, " Akwai yarjejeniya da muka yi da mahukuntan Saudiya inda muka ajiye wa'adin biyan kudin don gudanar da dukkan shirye-shiryen da suka dace, to idan mutum bai biya ranar 5 ga watan Fabrairu wadda itace ranar karshe ta biyan kudin, to sai dai a hadu a hajjin badi na 2026."

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT