KONEWAR MOTAR DOKON MAI FETUR: IGP YA JAJANTAWA GWAMNATI DA AL UMMAR JAHAR NEJA.
IGP Ya umurci dukkanin kwamishinonin Yan sanda da su inganta sashin rundunan dake kula da hatsura wato MTDs domin gudanar da aiyukan yadda ya kamata.
Babban sifeton Yan sanda Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D, NPM, ya mika ta aziyarsa ga gwamnati dama Al ummar jahar Neja biyo bayan hatsarin konewar wata tankar Mai Wanda ya faru jiya 18-1-2025 a mahadar hanyar da ya hada tagwayen hanyar Abuja-Kaduna da ake kira Dikko a jahar Neja, hatsarin ya farune a lokacin da Tankar dauke da Mai featur inda ta kinucewa direban lamarinda yasa ta kama da wuta lamarin yayi sanadiyar rasa rayuka 73, mutane da dama sun jinkata a yayinda shaguna da dama sun Kone.
Kakakin rundunan shelkwatan Yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Babban sifeton ya jaddada cewa Yana da muhimmanci a dauki dukkanin matakai da suka dace domin kula da kan hanyoyi domin kaucewa duk abinda zai kawo hatsura.
Saboda haka nema Babban sifeton ya umurci dukkanin kwamishinonin Yan sandan jihohi da su inganta sashin dake kula da hatsura wato MTDs dake jihohinsu tare Kuma da hada Kai da sauran hukumomin kare hatsura, domin tabbatar da ganin abi Ka idodin tuki a kan manyan hanyoyi dake fadin kasan nan, IGP ya kirayi masu ababen hawa da matuka ababen hawa da su tabbatar da lafiyar motocinsu tare Kuma da bin dokokin tuki domin kariya daga hatsari.
Babban sifeton ya yi a du ar Allah ya jikan wadanda suka tasu tare da Kiran masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada Kungiyoyin sifiri da ma Al umma da suma su bada tasu gudumawa tare Kuma da gudanar da aiyukansu yadda ya kamata domin ganin an samu saukin faruwa hatsura.
Comments
Post a Comment