KWAMISHINAN YAN SANDAN JAJAR ADAMAWA YA GABATAR WA SABBIN KURATAN YAN SANDA JAWABI INDA YA KIRAYESU DA SUKASANCE MASU MAIDA HANKALI WAJEN GUDANAR DA AIYUKANSU YADDA YA KAMATA.










Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris Psc(+), ya gabatarwa sabbin Jami an Yan sanda jawabi wadanda aka turosu jahar inda ya kirasu da sukasance masu gudanar da aiyukansu kamar yadda doka ya tanadar ksancewa shine farkon fara aiki a matsayin Yan sanda a Rundunan yan sanda Najeriya.




Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da aikewa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar.





Kwamishinan Yan sandan yayi wannan kirane a lokacin da yake yiwa sabbin Jami an Yan  sandan jawabi a shelkwatan rundunan Yan sandan dake kan titin Maishariya Buba Ardo inda ya shaida musu cewa da a da biyayya shine kashin bayan rundunan Yan sandan Najeriya. Ya ja hankalin sabbin Yan sandan da sukasance masu bin Ka idodin aiki tare da sauke nauyi da ya rataya akansu, da Kuma su kaucewa duk abinda zai kawo rarrabuwar Kai a rundunan Yan sandan a lokacinda suke gudanar da aiyukansu.




Gudanar da aiyukan daban daban a jahar Wanda hakan yasa ake diban Yan sanda harma da basu horo da Kuma yayesu daga kwakejin Yan sanda a jahar Birno da jahar Kaduna a ranan talata 23-1-2025.




Yaye sun na zuwa ne bayan diban sabbin Jami an yasanda dubu goma na kasa baki Daya a rundunan Yan sandan.





Kwamishinan yace yace wadanan sabbin Yan sandan za a turasu a kananan hukumominsu dake fadin jahar, Kuma hakan Yana daga aniyar Babban sufeton Yan sandan IGP Kayode Adeolu Egbetokin,ph,D,NPM's domin inganta kare Al umma dama inganta tsaro wa jama a da Samar da dabarun bada kariya.




Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT