RUNDUNAN YAN SANDA A JAHAR ADAMAWA TANA TSARE DA MUTANE BUYU DA AKE ZARGI DA YIWA WATA KARAMAR YARINYA FYADE. Rundunan Yan sandan jahar a Rana 24-1-2025 tayi nasaran cika hanu da mutane biyu da ake zargi da yiwa karamar yarinya fyade a Sangere Futy dake karamar hukumar Girei. Wadanda ake zargindai sune Bala Muhammed Dan shekara 35 da haifuwa, da Usman Abdullahi Mai shakekaru 17 da haifuwa dukkaninsu suna zaune ne Sangere Futy dake karamar hukumar Girei. Wadanda ake zargin dai tun a ranan 12-1-2025 sukayiwa yar shekara 11da yar shekara 14 fyade inda sukaita wasan buya da jami an tsaro Wanda sai a ranan 22-1-2025 akayi nasaran cafke su alokacin da rundunan ta samu korafi dangane da lamarin. Kwamishinan Yan sandan CP Dankwambo Morris , Psc,(+), daga samun rahoton ya tura Jami an Yan sandan dake aiki da ofishin Yan sanda dake Girei wadanda Kuma sune sukayi nasaran kama wadanda ake zargin. A yayin gudanar da bincike dukkaninsu sun amsa kaifinsu, indama suka ce bada gangan sukayi ba, kuskure ne aka samu Daya daga cikin wadanda ake zargin yace shedan ne yasa shi aikata haka. Kwamishinan Yan sandan ya tabbatar da cewa da zaran an kammala bincike kan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shariya. HAKAN NA KUNSHENE A CIKIN WATA SANARWA DAGA KAKAKIN RUNDUNAN YAN SANDAN JAHAR ADAMAWA SP SUKEIMAN YAHAYA NGUROJE. A MADADIN KWAMISHINA YAN SANDAN JAHAR ADAMAWA.








Rundunan Yan sandan jahar a Rana 24-1-2025 tayi nasaran cika hanu da mutane biyu da ake zargi da yiwa karamar yarinya fyade a Sangere Futy dake karamar hukumar Girei.




Wadanda ake zargindai sune Bala Muhammed Dan shekara 35 da haifuwa, da Usman Abdullahi Mai shakekaru 17 da haifuwa dukkaninsu suna zaune ne Sangere Futy dake karamar hukumar Girei.


Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



Sanarawan tace Wadanda ake zargin dai tun a ranan 12-1-2025 sukayiwa yar shekara 11da yar shekara 14 fyade inda sukaita wasan buya da jami an tsaro Wanda sai a ranan 22-1-2025 akayi nasaran cafke su alokacin da rundunan ta samu korafi dangane da lamarin.




Kwamishinan Yan sandan CP Dankwambo Morris , Psc,(+), daga samun rahoton ya tura Jami an Yan sandan dake aiki da ofishin Yan sanda dake Girei wadanda Kuma sune sukayi nasaran kama wadanda ake zargin.



A yayin gudanar da bincike dukkaninsu sun amsa kaifinsu, indama suka ce bada gangan sukayi ba, kuskure ne aka samu Daya daga cikin wadanda ake zargin yace shedan ne yasa shi aikata haka.



Kwamishinan Yan sandan ya tabbatar da cewa da zaran an kammala bincike kan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shariya.




Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT