Rundunan Yan sanda zata gudanar da Attisayen harbe harbe.







Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tana Mai farin cikin sanar da jama a cewa zata gudanar da ATTISAYEN harbe harbe da Jami anta wadanda ke yaki da ta addanci wato CTU Wanda  za a gudanar akan titin zuwa Mubi dake cikin karamar hukumar Girei.





Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Ana saran gudanar da harbe harben za afara a ranan laraba 15-1-2025 Wanda zai dauki yini Daya.




Saboda haka ana shawartan dukkanin mazuna yankin, ko masu gudanar da kasuwanci, matukan ababen Hawa, manoma da makiyaya, da su kaucewa wurin da za a gudanar da harbe harben.




An sanar da Al umma cewa an dauki dukkanin  matakai tsaro  da suka dace domin bada kariya.




HAKAN NA KUNSHENE A CIKIN WATA SANARWA DA KAKAKIN RUNDUNAN YAN SANDAN JAHAR ASAMAWA SO SULEIMAN YAHAYA NGUROJE YA SANYAWA HANU A MADADIN KWAMISHINA YAN SANDA.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE