An baiyana cewa Yan jarida suna taka mahimmiyar ruwa wajen Samar da zaman lafiya da cigaba.
An bukaci da Yan jarida sukasance masu gudanar da aiyukansu bil hakki da gaskiya da kuma sanya tsoron Allah a zukatansu domin samuna nasaran aiyukansu yadda ya kamata.
Dr Bashir Aliyu Imam Hong ne ya bada wannan shawara a lokacin da yake gabatar da lacca a wurin taron Ramadan Lecture Wanda kungiyar Yan jarida musulmai ta shirya Kuma aka gabatar a shelkwatar majalisar Addinin Musulunci dake Yola.
Dr Bashir Aliyu ya ja hankalin Yan jarida da su maida hankali wajen gudanar da aiyukansu domin a cewarsa suna da rawa da zasu iya takawa wajen Samar da hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin jama a, don haka Yana da muhimmanci Yan jarida sukasance masu yin taka tsantsan wajen aiyukansu.
Dr Bashir ya baiyana farin cikinsa dangane da shirya wannan taro Wanda acewarsa kungiyar wato MMPN ta taka rawan gaban hantsi don ko ba komai ta nuna cewa da gaske takeyi wajen yadda duk abinda zai daukaka addinin Musulunci.
Shima a jawabinsa tunda farko Alhaji Gambo Jika shugaban majalisar harkokin addinin Musulunci a jahar Adamawa, Kuma shinema shugaban taron ya yabawa kungiyar ta MMPN bisa shirya wannan taro, domin acewarsa shirya irin wannan taro zai taimaka wajen bunkasa tare da cigaban addinin Musulunci.
Ya shawarcesu da su Kara kaimi wajen gudanar da aiyukansu, tare dayin dukkanin abinda suka dace domin cigaban addinin Musulunci dama aiyukansu.
Mallam Malami Garba Shima jaddada kiransa yayi ga Yan jarida da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa tsarin doka, da Kuma kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin Al umma.
Ya Kuma jahankalin Yan jarida da kada su bari son duniya yasa su aikata abinda zai janyowa addinin matsala, ko tashin hankali.
Shi kuwa Dr Salihu Ateequ shawartan Yan jarida yayi musammanma wadanda ke amfani da shafukan zada zumunta da su maida hankali sosai akan aiyukansu domin samun cigaba.
A jawabinsa na maraba shugaban kungiyar ta MMPN a jahar Adamawa, Alhaji Shehu Aliyu yace manufar kungiyar dai I tace Samar da zaman lafiya, hadin Kai, a tsakanin Al umma musulmai dama sauran Al umma, baki Daya.
Kuma kungiyar a shirye take tayi dukkanin maiyiwa domin daidai yadda aikin jarida zan kasance a addinin Musulunci.
Harwayau Kungiyar ta rarrabawa marassa galihu da marayu kayakin abinci da suka hada da ahinkafa, gishiri, Maggi sama da mutane goma.
Taron ya samu halartan malamai daga sassa daban daban dake fadin jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment