An bukaci Al umma musulmai da su rubaiyya aiyukan ibada a wannan wata na Ramadan.





A yayinda ake cigaba da Azumin watan Ramadan an kirayi Al umma musulmai da sukasance masu maida hankali wajen yin ibada da kuyin adu o I domin samun tsira ranan gobe kiyama.




Shugaban makarmtar Sakandaren kimiya ta Sugu dake karamar hukumar Ganye a Jahar Adamawa Mallam Abubakar Hamman Tukur Tola ne ya bada wannan shawara a zantawaraa da manema labarai  a Ganye.




Mallam Abubakar Hamman Tukur yace watan Azumi watane da yake da muhimmanci ga Al umma musulmai don haka Yana da muhimmanci ga Al umma musulmai su Kara kaimi wajen bautawa Allah madaukakin sarki domin samun lada Mai yawa.




Mallam Abubakar ya kirayi Al umma musulmai musammanma masu hanu da shuni da su rinka taimakawa marassa galihu, harma da mabukata, domin suma su samu saukin rayuwa a tsakanin Al umma.




Ya Kuma Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na Azumi wajen yin adu o I domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin jahar dama kasa baki Daya.




Abubakar ya Kuma shawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da su marawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri baya domin ya samu damar gudanar da aiyukan cigaban jahar baki Daya 



Ya jinjinawa gwamna Ahmadu Fintiri bisa kokarinsa na bunkasa harkokin ilimi a fadin jahar, saboda haka ya kamata a bashi hadin Kai musammanma da yake biyan kudin jarabawan kammala sakandaren wato WAEC da NECO wannan abun a jinjina masane.




Don haka nema ya ke godewa gwamna Fintiri dangane da yadda yake maida hankali wajen tsaro, ilimi, kiwin lafiya, da dai sauransu.




Da wannan ne yake kira ga jamma a da su sanya gwamna cikin adu I insu domin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaba da ya sanya agaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT