An bukaci al ummar musulmai da rubaiyya aiyukan ibadarsu a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan.
An kirayi Al umma musulmai da su Kara kaimi wajen ibada musamman a kwanaki goma na karshen Ramadan domin samun Lada da Kuma tsira ranan gobe kiyama.
shugabar kungiyar Women In Da awa a jahar Adamawa Hajiya Rabi ce tayi wannan kira a sakonta da ta akewa manema labarai a Yola.
Hajiya Rabi tace kwanaki goma na karshen watan Ramadan suna da matukan muhimmanci ha Al umma musulmai don haka Yana da muhimmanci Al umma musulmai suyi amfani da wannan damar wajen ibadu da adu o I domin samun taimakon Allah a koda yaushe.
Hajiya ta sharci Al ummah Musulmai da su maida hankali wajen tallafawa marassa galihu, dayin Sadaka daku kautatawa Al ummah.
Ta yiwa Al umma musulmai fatan Alheri tare da yin Adu ar Allah madaukakin sarki ya karbi dukkan Ibadan da Al umma musulmai sukayi a cikin watan Ramadan.
Ta Kuma shawarci daukacin Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokacin wajen adu o I na musamman domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a jahar dama kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment