An bukaci shuwagabanin makarantun gaba da Firamare da su Kara himma wajen gudanar a aiyukansu.
An ja hankalin shuwagabanin makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa da aukasance masu sanya ido da Kuma yin hattara wajen gudanar da aiyukansu.
Mukaddashin Babban Sakataren Hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa, Birsan Penuel ne yayi wannan Jan hankali a lokacin da yake jawabi a wurin taron da ya gudanar da shuwagabanin makarantun gaba da Firamare a Makarantar Sakandaren Gwamnatin wato GSS Hong dake karamar hukumar Hong dake jahar Adamawa.
Mr Birsan Penuel yace ya kamata shuhabanin makarantu gaba da Firamare su maida hankali sosai wajen kula da aiyukan malamai dake karkashinsu domin a cewarsa ya lura wasu shuwagabanin makarantun suna sakaci wajen lura da aiyukan malamai Wanda Kuma hakan Yana kawo koma baya wajen karantarwan makarantun.
Mr Penuel ya shaidawa shuwagabanin da su mikawa hukumar sunan duk wani Malami da baya zuwa Makarantar ko Kuma baya shiga aji domin karantarwa Wanda acewarsa hakan zai basu damar daukan mataki akai.
Mr Birsan yace tunda gwamnatin jahar Adamawa da rarraba dukkanin kayakin karantarwa da suka dace saboda baiga wani dalilin da za ace Malami baya shiga ajiba.
Da wannannema yake godewa gwamnatin jahar Adamawa karkashin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na wadatar da kayakin karatu harma dana karantarwa a dukkanin makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar.
Ya Kuma tabbatar da cewa hukumar dake kula da makarantu gaba da Firamare zata tsaya akan kafarta domin ganin an baiwa dalube inganceccen ilimi.
Ya Kuma shawarci shuwagabanin makarantun gaba da Firamare da sukasance an samun kyakkawar halaka da hadin Kai a tsakanin shuwagabanin makarantun da Al umma harma da kungiyar Malai da iyaye wato PTA domin ganin daluben su samu inganceccen ilimi, yadda ya kamata.
Mr Birsan ya jajantawa karamar hukumar ta Hong bisa abinda ya fadu a wata Makarantar na matsarar tsaro, Yana Mai Adu ar Allah madaukakin sarki ya cigaba da kare malamai dama daluben a dukkanin makarantun dama Al umma baki Daya.
Shima a jawabinsa shugaban Makarantar ta GSS Hong Emmanuel Yarima yace sun gudanar da taron ne da zummar dubawa tare da warfare matsaloli dama kalubale dake fuskantar aiyukansu. Da Kuma zakulo hanyoyi da za a magancesu domin inganta aiyukansu.
Ya Kuma yaba tare da marabtar Babban sakataren Hukumar da ke kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa Mr Birsan Penuel, bisa kokari da yakeyi na ganin an inganta makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa.
Yarima yana Mai fatan cewa wannan taro zai zama silar samun hadin Kai da Kuma magance akasarin matsaloli da makarantun ke fuskanta.
Da suka nasu jawabi Mrs Ladi Vandy tare da Rubben sun baiyana farin cikinsu dangane da wannan taro, domin a cewarsu sun koyi abubuwa da yawa da zasu taimaka musu wajen Kara kaimin kula da makarantu da suke shugabanta domin samun cigaba.
Comments
Post a Comment