BIKIN SALLAH: kungiyar NUJ a jahar Adamawa ta taya gwamna murnan bikin karamar Sallah.
A yayinda ake gudanar da bukukuwar karamar Sallah shuwagabanin kungiyar Yan jarida a Najeriya NUJ shiyar jahar Adamawa suna masu taya gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, da mataimakiyarsa Farfesa kalatapwa Farauta, kakakin majalisar dokokin jahar da membobin majalisar dokokin jahar Adamawa, Dana majalisun gudanarwan jahar majalisar sarakunan jahar Adamawa, murnan bikin sallar wannan shekara.
Kungiyar ta baiyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun sakatarenta Mr Fidelis Jockthan a Yola.
Sanarwan tace ana gudanar da bikin ne saboda nuna kauna Yan uwa da abokan arziki da Kuma yin dukkanin abinda suka dace domin Samar da zaman lafiya hadin Kai harma da ziyarce ziyarcen Yan uwa.
Harwayau sanarwan ta kirayi daukacin Al umma musulmai da sukasance sunyi amfani da abinda suka koya a lokacin Azumin watan Ramadan.
Kungiyar ta NUJ a dokance zata cigaba dayin dukkanin abinda suka dace domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al umma, saboda haka akwai bukatan yin adu o I domin samun cigaba. Moron domokiradiyar da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ke gudanarwa a karkashin shugabancinsa.
A sanarwan anyi adu ar Allah madaukakin sarki ya karbi dukkanin adu o I da aKa gudanar, tare da neman amincewa da taya murnan daga shugaban kungiyar ta NUJ a jahar Adamawa dama membobin kungiyar.
Comments
Post a Comment