Hukumar dake kula da makarantu gaba da Firamare ta Sha alwaahin inganta karantarwa amakarantu dake fadin jahar.
A wani mataki na inganta kowarwa a jahar Adamawa, Hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa ta Kai ziyaran bazata a Makaranta sakandaren gwamnati na jeka Ka dawo wato GDSS Bachure.
Mukaddashin Babban sakataren Hukumar Mr Birsan Penuel ne ya jagoranci tawagan hukumar domin Kai ziyaran domin ganewa idonsu yadda ake gudanar da aiyukan karantarwan a Makarantar.
Da yake zantawa da manema labarai jikan bayan Kai ziyaran Mr Birsan Penuel yace da farko ya godewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa dangane da wannan dama da ya basu ma kula da makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa domin ganin an samu damar bunkasa illimin a tsakanin Al ummar jahar.
Mr Birsan Penuel ya Kuma baiyana cewa dalilinsu na Kai ziyaran baza ta a makarmtar shine domin duba yadda malamai ke gudanar da aiyukansu domin a cewarsa in ba matakin haka aka daukaba wasu makamai zasu rinka zaman a inuwar bishiya ba za su maida hankali wajen karantarwaba.
Saboda haka daukan irin wannan mataki zai taimaka sosai wajen yadda malamai zasu maida hankali kan aiyukansu yadda ya kamata.saboda haka nema ya je Makarantar domin dubasu saboda haka karsuce ba a sanya musu ido.
Mr Birsan ya baiyana cewa yake Kuma ya dubi littafin rijistan malamain da suke zuwa Makaranta dama wadanda basa zuwa Makaranta Kuma ya fahinci cewa wasu suna zuwa wasu Kuma basa zuwa.
Mr Penuel ya Kara da cewa Yana Mai Jan hankalin malamai da sukasance suna maida hankali kan aiyukansu, domin baza a lamuncewa duk malamin da baya zuwa makarantaba, don duk malamin aka samu da laifi za a hukuntashi don ya zama izzina ga sauran.
Babban sakataren ya ja hankalin malamai da su Kara himma da Kuma su sani wannan alkawarin ne da suka dauka tsakaninsu da Allah Kuma riban karantarwa Yana ga yaran harma da albarkansu, saboda haka ya zama wajibi su maida hankali sosai wajen karantarwa.duba da yadda gwamnati ta wadatar da kayakin karatu a makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa.
Ya Kuma kirayi iyaye da suma su bada nasu gudamawa ta marawa gwamnatin jahar Adamawa baya domin ta samu nasaran cimma burinta na bunkasa illimi a fadin jahar baki Daya.
Ya shawarci iyaye da su maida hankali wajen tura yaransu Makaranta akan lokaci, su Kuma maida hankali kan yaransu kar su bar yaran suna gararanba akan tituna su kasance suna kula da harkokin su yadda ya kamata.
Ya Kuma jadda da kiransa ga iyaye da su marawa gwamnati baya ta yadda gwamnatin dake biyawa yaran kudin jarabawan kammala sakandaren wato WAEC da NECO saboda haka akwai bukatan baiwa gwamnati hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na baiwa yara illimi Mai inganci a fadin jahar.
A karshen Babban sakataren ya godewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na wadatar da makarantun gaba da sakandare da kayakin karatu Wanda acewarsa hakan damace ga Al ummar jahar Adamawa na samun illimi yadda yakamata.
Comments
Post a Comment