Hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa da Sha Alwaahin aiwatar da tsarin gwamna Fintiri akan harkokin illimi a fadin jahar.
Daga An Nur Hausa.
Hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa, wato Adamawa post primary schools management Board a turance, karkashin jagoranci Mr Birsan Penuel, Tasha alwashin inganta makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa.
Babban sakataren hukumar dake kula da makarantu gaba da Firamare Mr Birsan Penuel ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na bada dukkanin kayakin karatu a makarantu dake fadin jahar Adamawa domin bunkasa ilimi a fadin jahar.
Ko a kwanan nanma Babban sakataren ya jagoranci rarraba kayakin karantarwa ga shuwagabannin makarantun gaba da Firamare da ya wakana a Makarantar GMMC dake nan Yola, da suka hada da Alli, takartun sakamokon. Jarabawar dalube harma da takardan tsarin karantarwa a wani mataki na inganta karantarwan makarantun baki Daya.
Babban sakataren Mr Birsan Penuel ya ja hankalin shuwagabanin makarantun gaba da Firamare da sukasance masu kyautata halaka tare da hadin Kai a tsakanin malamai da iyayen dalube Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen Samar da inganceccen ilimi a tsakanin dalube dake fadin jahar.
Mr Birsan Penuel ya baiyana cewa dolene a yabawa gwamna Fintiri domin ya inganta sashin illimi a fadin jahar, bayan ga bada ilimi kauta gwamna ya wadatar da makarantu da kayakin aiki da zai baiwa malamai damar karantar da yara yadda ya kamata
Ya Kuma tabbatar da cewa hukumar ta Post Primary schools management Board baza tayi kasa a gwiwaba wajen maida hankali akan makarantun gaba da Firamare domin ganin sun aiwatar da manufa gwamna Fintiri na bunkasa harkokin illimi a fadin jahar.
Baya ga kwamtin daban daban dake zagaya makarantun Mr Birsan Penuel da kansa Yan ziyartan makarantun domin ganewa idonsa yadda ake gudanar da aiyukan makarantu dama yadda ake karantarwa a makarantun, tare da Jan kunnen malamai da su maida hankali wajen karantarwa domin hukumar baza ta lamunta da hali ko inkula da wasu malamai keyiba don ya zama wajibi a dauki dukkanin matakai da suka dace.
A baya bayan nan dai Mr Birsan Penuel ya ziyarci makarantu da suka hada da Bachure, Technical, dake Yola, Jaboliyo, Modibbo Raji dake cikin garin Yola, Doubeli government day secondary school, Demsawo secondary school, da Capital secondary school, da dai sauransu,
Mr Birsan Ya baiyana cewa tunda yazo hukumar a matsayin Babban sakatare na riko bai tsaya da wasaba wajen maida hankali ga makarantun gaba da Firamare dake fadin jahar Adamawa domin tabbatar da ganin komai ya tafi daidai ba tare da wasu matsaloliba, da Kuma kaucewa duk abinda zai kawowa makarantun tarnaki a wajen gudanar da aiyukansu.
Kawo yanzu dai Mr Penuel yace duk da cewa ana Dan samu matsaloli nan da can amman an samu raguwar matsaloli da dama sakamokon yadda yake Kai ziyaran a makarantun domin ganin komai ya tafi dai dai Kuma dalube sun samu ilimin da ya kamata.
Babban sakataren yace gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri tayi kokari sosai a bangaren illimi, baya ga baiwa dalube illimi kauta, gwamnatin ta rarraba kayakin karatu, harma da inganta tsaro a dukkanin makarantu dake fadin jahar Adamawa, domin baiwa malamai da dalube damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata ba tare da wata matsalaba.
A yanzu haka dai Mr Birsan Penuel Yana cigaba da ganawa da shuwagabanin makarantun gaba da Firamare dama masu ruwa da tsaki a bangaren illimi domin dubawa da zakulo hanyoyin da za a magance duk wasu kalubalen dake fuskantar makarantun.
Saboda haka nema yake kira ga daukacin al ummar jahar Adamawa da su baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu nasaran inganta harkokin illimi a fadin jahar Adamawa.
Ya Kuma tabbatar da cewa hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare tana aiki ba kama hanun yaro domin ganin yara sun samu nagarceccen illimi domin samun cigaban harkokin illimi, harma da wanzar da zaman lafiya.
Ya Kara kira ga jama a da sicigaba dayin adu o I domin neman taimakon Allah wajen kawo ga karshen matsalar tsaro a jahar dama kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment