Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta gano wasu shanu da ake zargin satosu akayi.
A kokarinta na yin sintiri domin kariya tare bankado aiyukan laifuka, Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta gano wasu shanu da aka sacesu.
Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
A yanzu haka Rundunan tana rike da shanun domin gudanar da bincike, Kuma da zaran an kammala bincike za a mikasu ga masu shi yadda ya kamata.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa *CP Dankwambo Morris psc(+),* ya kirayi Al umma musamman wadanda shanunsu suka bata ko aka sace, da sukai rahoto a ofishin Yan sanda dake Numan da cikekken shaidar mallakar shanun domin karba.
Comments
Post a Comment