Yanayin Zafi: An bukaci makarantu su maida hankali wajen baiwa dalube kariya daga cuttuka.






 An shawarci shuwagabanin makarantu musammanma na kwana da su maida hankali sosai a dakunan kwanan dalube domin Samar musu da yanayi Mai kyau a wanan lokaci na zafi domin kaucewa kamuwa da cututtuka.





Babban sakatare a hukumar hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa, Mr Birsan Penuel ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Mr Birsan Penuel ya baiyana cewa Kiran ya zama wajibi duba da yanayin da ake ciki a halin yanzu na zafi, to ya zama wajibi a sanarwa dalubai wuraren kwana Mai inganci da zai kasance ana samun iska a Koda yaushe domin ganin an kula da ingancin lafiyar daluben a makarantun.




Babban sakataren ya kirayi shuwagabanin makarantu da su kaucewa Tara dalube a wuri Daya sukasance masu lura da yanayin zafin domin ganin daluben sun samu kula da ta dace.




Mr Birsan ya Kuma shawarci dalube da suma su maida hankali wajen cinkusuwa a wuri Daya sukasance masu maida hankali wajen inda babu zafi domin gudanar da aiyukansu na karatu.





Ya Kuma yabawa gwamnatin jahar Adamawa dangane da na mijin kokari da takeyi na inganta ilimi dama daluben baki Daya.



A kwanan nan ne dai hukumar asaahen a Najeriya wato Mimet ta fitar da sanarwan cewa za a fuskanci yanayin zafi a Najeriya, saboda haka a maida hankali wajen kula da lafiya domin kaucewa kamuwa da cututtu da ake kamuwa da su a lokacin zafi.




Ko majalisar wakilain tarayyar Najeriya a makon da ta gabata ta fitar da sanarwa baiwa gwamnatin umurnin kula da makarantu dake fadin Najeriya da Kuma basu kariya domin kaucewa jarbuwar cututtuka.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT