An kaddamar da baiwa manoma iri a jahar Adamawa.

 






Gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umar Fintiri ya kaddamar da bada iri ga manoma da zasu Nomi iri da za a shuka a noma na gaba wato foundation seeds a turance domin bunkasa harkokin noma a fadin jahar.





Da yake kaddamar da bada iri a dandalin mahmudu Ribadu dake Yola karkashin hukumar bunkasa kasuwanci kayakin noma ADAS tare da hadin gwiawar IITA da IsDB domin bunkasa tare da inganta harkokin noma a fadin jahar baki Daya.






Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda kwamishinan Al barkarun noma Farfesa David Jatau ya wakilta ya baiyana godiyarsa da farin cikinsu dangane da wannan na mijin kokari da akayi na rarrawa manoma iri.






Ya Kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa zata cigaba da yin dukkanin maiyiwa domin ganin an samu cigaba a harkokin noma a fadin jahar. Don haka nema ya kirayi manoma da sukasance masu baiwa gwamnati hadin Kai da goyon baya domin ta samu nasaran cimma burinta.





Da yake nashi jawabi ko odinaton kungiyoyin IITA da IsDB Muhammed Ahmed yace sukasance a jahar Adamawa ne domin taimakawa manoma a fadin jahar domin basu damar bunkasa harkokin nomansu na tare da wata matsalaba.




Ya Kuma kirayi manoma da Maida hankali wajen yin amfani da abinda aka basu yadda ya kamata domin ganin sun samu nasaran cigaban aiyukansu.






Ja mi in aiyukan hukumar ADAS Yunusa Ibrahim yace hukumar ta lashi takwabi bunkasa harkokin kasuwancin harkokin kayakin noma domin ganin an samu cigaba noma harma da Samar da aiyukansu.





Shi kuwa shugaban masu noma iri a jahar Adamawa Mallam Sahabo Baba ya yaba da yadda aka kaddamar da tsarin Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen samun cigaban aiyukansu na Samar da iri.





Ya jadda da aniyarsa na ganin an bunkasa harkokin Samar da Iruka a fadin jahar Adamawa domin samun cigaban manoma a ciki da wajen jahar Adamawa.





Hakimin cikin garin Jimeta Muhammed Cibado ya baiyana godiyarsa da Jin dadinsa dangane da yadda ake sumu iri a fadin jahar Adamawa Wanda acewarsa hakan cigabane.





Ya shawarci manoma da suyi amfani da kayakin da aka basu dama ilimi da aka basu domin samun cigaba.




Kungiyoyin manoma dabab daban da suka hada da na manoman shinkafa RIFAN, Dana manoma masara MA AN, NECAS, da dai sauransu duk sun jalarci Taron.





Manoma 501 wadanda suka fito daga kungiyoyi 41 dake cikin kananan hukumomin 8 ne dai suka amfana da kayakin iri da Kuma taki, Wanda kowannensu ya samu iri Mai nauyin KG 25 walau na shinkafa ko na masara.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT