An shawarci Al umma Musulmai da su rinka anfani da watanin addinin musulunci.
An kirayi Al umma Musulmai da sukasance suna Maida hankali wajen aikin da watannin addinin musulunci a dukkanin lamuramsu, domin samun cigaban addinin musulunci.
Shugaban majalisar addinin musulunci dake karamar hukumar Mubi a jahar Adamawa Mallam Danmama Umar ne ya bada wannan shawara a zantarwarsa da manema labarai a Yola, fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Mallam Danmama Umar ya baiyana cewa yin amfani da watannin addinin musulunci yana da matukan muhimmanci saboda haka ya kamata Al umma Musulmai sukasance suna amfanin da kaladar ta addinin musulunci a Koda yaushe domin samun cigaba.
Da wannan nema yake kira ga makarantun islamiyoyi da suksance suna nunawa yaran muhimmanci kalandar addinin musulunci tun suna yara, Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen ganin an cigaba da yin amfani da watannin addinin musulunci yadda ya kamata.
Danmama Umar ya shawarci malamai musammanma masu WA Azi da sukasance suna wayarwa Al umma Musulmai Kai dangane da yin amfani da kalandar addinin musulunci a Koda yaushe.
Ya Kuma yabawa majalisar addinin musulunci a matakin jahar karkashin jagorancin Alhaji Gambo Jika bisa kokarinsa na kaddanar da kalandar addinin musulunci a kowace shekara, wannan acewarsa wannan cigabane sosai, saboda yana da muhimmanci a marawa majalisar baya domin ta samu nasaran gudanar da aiyukanta yadda ya kamata.
Ya kara da shawartan iyaye da Suma suna da rawa da zasu iya takawa wajen nunawa yaran yin amfani da kalandar addini musulunci.
Comments
Post a Comment