Antsinci Wani yaro Dan jahar Adamawa a jahar Kaduna.
MUHAMMAD ABUBAKAR Mai shekaru 8 da haifuwa, a takaice dai an sanar da batansa tare da samunsa.
Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Yace shi Dan jahar Adamawa ne Wanda aka kaishi jahar Kaduna domin yin karatun addinin musulunci, Amma yanzu an sameshi a garin Kudaru dake karamar hukumar lere a jahar Kaduna.
Yaron yace iyayensa suna zaune a ta wajen filin wasa na wucin gadi, wato temporary stadium, dake cikin garin Jimeta cikin karamar hukumar Yola ta arewa, a jahar Adamawa.
Ana rokon duka Wanda Allah yasa ya san iyayensa ko yasan wadanda suke halaka da yaron ya tuntubi osfishin kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa ko Kuma Alhaji Tukur Zubairu dake jahar Kaduna ta wadan Nan number wayoyi. 08136544154.
09015595292.
Comments
Post a Comment