Gwamna Fintiri Ya Kai Ziyara Ga Yara 13 da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Yara, Ya Ba da Tallafi
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya kai ziyara ga yara 13 'yan asalin jihar da aka ceto daga hannun masu safarar yara.
Gwamnan, wanda mataimakinsa ya wakilta tare da rakiyar Shugaban Karamar Hukumar Yola North, ya nuna kudirin gwamnatin jihar na kula da walwalar yaran da aka ceto.
Yaran da lamarin ya rutsa da su suna karɓar kulawar lafiya a Asibitin Musamman na Yola, inda ake basu magani saboda radadin da suka sha.
A matsayin nuna jin ƙai da goyon baya, gwamnatin jihar ta ba kowane yaro kuɗi da kayan abinci. Mataimakin Gwamna, a madadin gwamnatin, ya mika tallafin kuɗi da kayan agaji domin tallafa wa yaran da iyalansu a lokacin murmurewa daga wannan ibtila’in.
A lokacin taron, Sakatare na Karamar Hukumar Yola North, Maulud Ishaq, ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali, yana kuma kira ga jama’a da su ƙara saka ido tare da haɗa kai domin hana irin wannan faruwa a gaba.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargi da safarar yaran ne a unguwar Jambutu ta jihar, yayin da yake ƙoƙarin kaisu gabashin ƙasar nan.
Maulud Ishaq – Sakatare na Karamar Hukumar Yola ta arewa dake jahar Adamawa ya nuna farin cikinsu dangane da ceto yaran.
Comments
Post a Comment