Kungiyar Tsangaya a jahar Adamawa ta bigi kirjin inganta karantarya, tsangaya a fadin jahar.
Kungiyar Tsangaya a jahar Adamawa tasha alwashi inganta tsarin karantarwar Tsangaya domin samun cigaban ilimin Tsangaya harma da na zamani.
Shugaban kungiyar a jahar Adamawa Abdulwahid Ibrahim ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar An Nur Hausa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Abdulwahid Ibrahim yace kungiyar tana iya kokarinta domin kulla halaka da gwamnati domin fadakar da gwamnatin matsayin Tsangaya, domin kaucewa dangantasu da masu aikata ba daidaiba ko wasu akidu da basu daceba.
Abdulwahid yace ko a yanzuma akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suke taimakawa kungiyar ta basu damar karantun zamani Wani lokacinma harda yunifom da dai sauransu.
Ibrahim ya Kara da cewa gwamnati itama tana tallafawa a wasu bangare musammanma ta bullo da karatun zamani a tsangayoyi da kungiyar ke da su domin ganin Suma sun tafi dai dai da zamani domin samun cigaba.
Yace kungiyar ta bigi girjin ganin ta tsafcace karantarwan Tsangaya Wanda hakan yasa suka dauki matakin ganin duk Wanda zai tura dansa karatun Tsangaya dolene ya rinka sanin halinda dansa ke ciki ba kamar yadda akeyi ada a rinka barinsu Kara zube, saboda haka dokene uba ya ringa ziyaryan dansa a Koda yaushe domin sanin yanayin da yake ciki.
Shugaban yace kungiyar zatayi dukkanin abinda suka dace domin fadakar gwamnatin dama Al umma cewa masu karatu a tsangaya Suma Yan kasa ne don haka Suma suna bukatar duk Wani taimako da ya kamata ayi musu domin samun cigaban kungiyar yadda.
Ya Kuma baiyana cewa baya ga kungiyoyin da suke basu hadin Kai gwamnatin ma tana iya kokirinta wajen inganta karatun tsangaya, Wanda Kayo yanzu Al umura sun fara dai dai ta.
Abdulwahid ya kirayi shuwagabanin kungiyar da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe domin samun cigaban kungiyar harma da wanzar da zaman lafiya a tsakanin kungiyar dama jahar baki Daya.
A Karshe ya kirayi daukacin Al umma da su Maida hankali wajen yin adu o I domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki ya kawo Karshen kalubalen tsaro a jahar dama kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment