Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta fara binciken dangane da harsashin da ya sami Jami in hukumar kwastom.













Rundunan Yan sandan jahar Adamawa a yanzu haka ta fara bincike kan zargin da harbin harsaahi da ya samu kami in kwastom wato Ibrahim Usman Mai shekaru 35 dake Mujara cikin karamar hukumar Mubi ta kudu, Wanda ake zargin rundunan aintirin hukumar kwastom din ne da harbashi.





Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.







Lamarin ya farune a ranan 16-7-2025 da misalin karfe 1600hrs. Biyo bayan samun kiran offishin Yan sanda dake jami ar jahar Adamawa wato ADSU dake Gude, Wanda hakan yasa DPO ya jagoranci tawagan Kai daukin gahgawa zuwa wurin, inda aka garzaya da mutumin zuwa Asibitin tarayya dake Mubi wato FMC Mubi, inda daga bisani Rai yayi halinsa.




Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris psc(+), ya baiyana cewa hukumomin hukumar kwastom na jiran cikekken bayani daga sashin binciken manyan laifuka CID bayan kammala bincike da Kuma bada rahoto.




Rundunan tana Mai tabbatar WA Al umma cewa za agudanar da adalci a yayin binciken Kuma za a sanar da dukkanin abinda ya faru.




Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT