Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta ceto yara sha uku da ake zargin an safaransu daga jahar Adamawa zuwa jahar Anambara.
Daga Alhassan Haladu.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta samu nasaran kama mutane 567 bisa zarginsu da aikata laifuka daban daban Wanda suka hada da yin garkuwa da mutane, kwacen wata, fashi da makami, safaran Yara da dai sauransu.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ne ya baiyana haka a lokacinda yake yiwa manema labarai jawabi dangane da aiyukan rundunan a shelkwatan rundunan dake Yola.
Dankwambo Morris yace cikin wadanda aka kama akwai Mrs Ngozi Abdulwahab yar shekaru 43 Wanda ke zaune a anguwar Jambutu a jahar Adamawa, da Mrs Uche Okoye yar shekaru 55 dake zaune a jahar Anambara, ana zarginsune da sarafan Yara daga jahar Adamawa zuwa jahar Anambara.
Rundunan ta Kuma ceto Yara Sha uku da akayi sarafansu da Kuma mutane hudu da akayi garkuwa da su, tare da gano makamai wasu kayaki irinsu mota, keken Napep, tv, kwanfita, da dai sauransu a wajen wadanda ake zargin.
Kwamishinan Yan sandan yace sun samu nasaran gudanar da wannan aiyuka ne tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, Yan sa Kai da dai sauransu.
Dankwambo ya sake jaddada aniyar rundunan na cigaba da baiwa Al umma kariya da Kuma yaki da aikata laifuka a fadin jahar domin ganin an samu cigaban zaman lafiya Mai daurewa.
Ya Kuma yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa goyon baya da yake baiwa rundunan a Koda yaushe Wanda hakan yana taimakwa rundunan sosai wajen samun nasaran aiyukanta.
Haka kazalika kwamishinan ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da su cigaba da baiwa rundunan hadin Kai da goyon baya da kuma Bata bayanai sirri da zai taimaka wajen dakile ta addanci a fadin jahar.
Rundunan ta Kara da cewa dazaran ta kammala bincike kan wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shariya.
Yara Sha uku da akayi safaransu kuwa da zaran an kammala duba lafiyarsu za a mikasu ga iyayensu.
Comments
Post a Comment