An nada Alhaji Baba Sahabo a matsayin maijimillar riko na Namtari Gurel,
Daga Alhassan Haladu Yola.
Majalisar masarautar jahar Adamawa ta nad Alhaji Baba Sahabo a matsatin Maijimillan Namtari Gurel na riko dake gundumar Namtari.
Nadin na zuwane bayan dakatar da Maijimillan na Namtari Gurel Mallam Kabiru Bobboi.
Wannan na kunahene a cikin wata takarda daga Sakataren majalisar masarautar jahar Adamawa Alhaji Umar Yahaya, Wanda yace nadin zai fara aikine daga ran 29-7-2025, har zuwa lokacinda majalisar za ta dauki mataki na gaba.
Majalisar masarautar ta Kuma shawarci Alhaji Baba Sahabo da ya gudanar da aiyukansa da gaskiya, zaman lafiya, hadin Kai, da Kuma tsoron Allah domin samun cigaban Namtari Gurel da Gundumar Namtari dama jahar baki Daya.
Comments
Post a Comment