An nemi da gwamnati ta tallafawa manoma da kayakin noma Mai raugwame domin bunkasa harkokin noma.

 









Daga Alhassan Haladu Yola.


Àn bukaci da gwamnatin tarayya ta Maida hankali wajen yiwa manoma rangwamen kan kayakin da suke amfani da su domin su samu damar bunkasa harkokin noma a fadin Najeriya.




Shugaban kungiyar Yan kasuwar arewacin Najeriya Alhaji Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a zantarwarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.





Alhaji Ibrahim 86 yace kawo yanzu kayakin abinci farashin kayakin abinci Yana sauka. Amma Kuma kayakin noma baya tabuwa saboda tsada da yayi don haka akwai bukatan yiwa manoma rangwamen kan kayakin da suke amfani da su a gonakainsu.





Alhaji Ibrahim ya baiyana cewa yawaitan kayaki ne yasa ake samu saukin kayaki Kuma karancinsa shine yake kawo tsadan kayakin, saboda haka a yanzu an samu yawaitan kayakin abinci shiyasa ake samun saukin kayakin abinci.






Sai dai Wani hanzari ba guduba kayakin da ake amfani da su wajen noma kayakin abinci yayi tsada saboda haka dolene gwamnati ta shiga tsakani domin taimakawa manoma da kayakin noma masu saukin farashi domin su samu kwarin gwiwar cigaba da harkokin noma yadda ya kamata.





Ya Kara da cewa Yanzu ana saida buhun taki dubu 70 da dubu50 Wanda hakan Yana kawo koma baya wajen gudanar da harkokin noma, Wanda Kuma sai Nan gabane za aka illar wannan matsalar.



Don haka ya kamata gwamnatici da masu ruwa da tsaki da suyi dukkanin Mai yiwa domin daukan mataki wajen magance matsalar baki Daya.




Alhaji Ibrahim ya Kuma jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jahar Adamawa, tare da yin Adu ar Allah madaukakin sarki ya kare na gaba ya Kuma mayar musu da abinda suka rasa, tare da shawartan dukkanin masu noma a gaban kokuna ko gidaje akan hanyar ruwa da su kasance masuyin taka tsantsan da Maida hankali kan abinda masana ke cewa domin samun tsira.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT