An shawarci gwamnatin tarayya Dana jihohi da su tallafawa manoma dake yankin Arewa masau gabas.
By Alhassan Haladu Yola.
An kirayi gwamnatin tarayya Dana jihohi da su gagauta taimakawa manoma dake yankin Arewa masau gabashin Najeriya da kayakin noma masu rangwame domin bunkasa da Kuma inganta harkokin noma saboda Samar da wadacecen abinci a yankin.
Masani kan harkokin noma a yankin na arewa masau gabas Alhaji Usman Suleiman Palam ne yayi wannan kira a zantarwarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Inda ya baiyana cewa yankin na arewa masau gabas ma fiskantar kalubale da dama wadanda suka hada da hauhawan faraahin taki magungunan feshi da dai sauransu.
Alhaji Usman Suleiman Palam ya Kara da cewa yanayin da ake cikin a yanzu akwai matsalar karancin abinci Dana tattalin arziki Wanda Kuma ba yankin kadaiba harma da kasa baki Daya. Don haka nema ya kirayi hukumomi a dukkanin matakai su wadatar da manoma da taki magungunan feshi cikin rangwame, da Inganceccen iri dama sauran kayakin aiki da zai taimakawa manoma wajen bunkasa aiyukansu domin Samar da cigaba dama bunkasa tattalin Arziki.
Kalubale dake fiskantar manoma a yankin na arewa masau gabas akwai bukatar gwamnati ta shiga ta samarwa manoma rangwame da Inganceccen iri, tsaro da dai sauransu.
Ya Kuma baiyana cewa taimakawa manoma abune da yake da muhimmanci don zaitaimakawa matasa wajen Samar da aikinyi inganta tattalinArziki, saboda acewarsa ya kamata masu ruwa da tsaki sukasance masu hada Kai wajen karawa manoman kwarin gwiwa, domin Suma suna da rawa da zasu iya takawa wajen cigaban harkokin noma.
Alhaji Palam ya kirayi Yan Najeriya da su cigaba da rungumar harkokin noma Wanda acewarsa hakan zai kawo zaman lafiya, dogaro da Kai, tare da bunkasa tattalin Arziki a fadin kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment