Gidauniyar HUG ya taimakawa mata 30 domin sana ar dogaro dakai a karamar hukumar Yola ta kudu.
Gidauniyar Hamidu Umaru Gulak Wanda akafi sani da HUG. Ya taimakawa mata akalla talatin a cikin karamar hukumar Yola ta kudu dake jahar Adamawa da kudaden sana o I domin su dogara da kansu da iyalensu dama Al umma baki Daya.
Gidauniyar ya fahinci cewa akwai bukatan karfafawa matan domin su bunkasa harkokin kasuwancinsu domin rage musu radadin wahalar rayuwa da suke cikin duba da yadda ake samun matsalar rayuwa a fadin kasan nan.
An zakulo wadanda suka cigajiyar Shirin daga cikin Al ummomin dake cikin karamar hukumar Yola ta kudu wadanda suka samu taimakon kudade da suka kama daga dubu 20,000 da 30,000 da kuma dubu 50,000 wanda acewarsu hakan zai taimaka musu na tsawon lokacin da Kuma bunkasa musu kasuwancinsu.
Da yake yiwa wadanda suka ci gajiyar Shirin Mudas Mai Karfe Wanda malami ne a jami ar modibbo Adama yace nan gaba ma za a taimakawa manoma. Inda ya kirayi wadanda suka amfani da taimakon da suyi amfani da shi yadda ya kamata domin samun cigaba.
Daya daga cikin wadanda suka amfana Hindatu Yunusa daga Bole lakkare Wanda ta nuna farin cikinta dangane da wannan taimako da ta samu ta Kuma yabawa gidauniyar na Hamidu, tare da tabbatarwa gidauniyar cewa zasuyi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace domin samun cigaban kasuwancinsu.
Ta baiyana cewa da wannan jari da ta samu zatayi amfani dashi ya wajen sayan gawayi tana sayarwa. tace ta Dade tana jiran abinda zata dogara dashi da iyalenta harma yace da wannan zata taimakawa mijinta don haka tana Mai godiya da wannan taimako.
Ta Kuma Kara da cewa wadannan kudade da suka samu daga gidauniyar na HUG, zai taimaka musu wajen inganta kasuwancinsu harma da bunkasa tattalin arziki.
Itama anata bangaren Zainab Umar wanda suka fito daga GRA dake cikin garin Yola. Tace wannan kudin da gidauniyar ya Bata zai zama silar inganta rayuwarta.
Gidauniyar dai ya gudanar da irin wadannan taimako a bangarori daban daban harma da aiyukan jinkai saboda haka gidauniyar ke godewa bisa hadin Kai da yake samu, Kuma da yardan Allah zai cigaba da aiyukan taimakawa.
Comments
Post a Comment